Miyagun 'Yan Bindiga Sun Sace Fasinjojin Motocin Gwamnatin Jihar Benue

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Sace Fasinjojin Motocin Gwamnatin Jihar Benue

  • Wasu 'yan bindiga sun tare motocin gwamnatin jihar Benuwai, sun yi awon gaba da fasinjoji aƙalla 10
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne a yankin Okene na jihar Kogi yayin da motocin Benue Links 2 ke hanyar zuwa Legas
  • Ma'aikatan kamfanin sufurin sun tabbatar da faruwar lamarin amma har yanzu ba bu sanarwa daga yan sanda a hukumance

Jihar Benue - Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji aƙalla 10 da ke hanyar zuwa Legas a cikin motocin bas guda biyu na kamfanin sufuri mallakar gwamnatin jihar Benuwai, Benue Links.

Matafiyan sun faɗa hannun miyagun 'yan bindigan ne a yankin Okene da ke jihar Kogi bayan sun baro Makurdi, babban birnin jihar Benuwai sun nufi jihar Legas.

Yan bindiga sun tare motocin gwamnatin Benue.
Miyagun 'Yan Bindiga Sun Sace Fasinjojin Motocin Gwamnatin Jihar Benue Hoto: Timothy Vihinga
Asali: Facebook

Ganau sun bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Lahadi da ta gabata bayan 'yan bindigan sun tare Motocin kamfanin sufurin gwamnatin Benuwai.

Kara karanta wannan

Hatsarin Kwale-Kwale a Neja: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 30, NSEMA

Wakilin jaridar Daily Trust ya tattaro cewa maharan sun yi garkuwa da mutane 10 a harin yayin da wasu da dama kuma aka ce sun tsere cikin daji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kuma bayyana cewa lamarin ya faru ne tsakanin karfe 2:00 na rana zuwa karfe 3:00 na yammacin ranar Lahadi a kan titin Ajaokuta/Okene.

Wani jami'in kamfanin sufurin Benue Links wanda ya nemi a ɓoye bayanansa saboda ba shi da hurumin magana kan batun, ya tabbatar da lamarin ga 'yan jarida ranar Litinin da daddare.

Ya ce:

"Motoci biyu lamarin ya shafa kuma mutane 10 aka sace daga ciki, tuni aka kai rahoton abinda ya faru caji Ofis ɗin Adogo kusa da Okene."

Wane mataki hukumar 'yan sanda ta ɗauka?

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) ta Kogi, SP William Aya, ya ce “Na lura, zan dawo gare ku,” a martanin da ya aike wa sakon da aka tura masa ta wayar tarho kan lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Kawo Motocin Da Za Su Rika Daukar Mutane Kyauta Saboda Tsadar Fetur

Amma har yanzun kakakin 'yan sandan bai yi ƙarin bayani kan harin ba har kawo yanzu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kwararren Akanta, Akintola Williams, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin kuma Masanin harkokin da suka shafi Akanta, Akintola Williams, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 104 a duniya.

Marigayin, wanda shi ne ɗan Najeriya na farko da ya zama kwararren Akanta na duniya, ya mutu wata ɗaya bayan bikin kara shekararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel