Tinubu Bai Ji Dadin Abin da Sojoji Suka Yi ba, Ya Tara Manyan Hafsoshin Tsaro a Aso Rock
- Shugaba Bola Tinubu ya tara manyan hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan kuskuren da sojoji suka yi a kasuwar Jilli
- Rahotanni sun nuna cewa bama-baman da jirgin sojoji ya saki a kasuwar sun yi sanadin mutuwar mutane fiye da 200, wasu da dama sun jikkata
- Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ya tirke duka masu ruwa da tsaki kan tsaro domin jin ainihin abin da ya faru da matakin da aka dauka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wani muhimmin taron tsaro tare da shugabannin rundunonin tsaro da Sufeto Janar na ‘yan sanda a fadarsa da ke Abuja.
Taron ya biyo bayan harin sama da sojojin Najeriya suka kai bisa kuskure a kasuwar Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe.

Kara karanta wannan
"Ina dalili": Gumi ya nemi majalisa ta duba yawan kashe fararen hula da sojoji ke yi

Source: Twitter
Bola Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro
Daily Trust ta ce rahotanni sun nuna harin ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 200, ciki har da fararen hula, yayin da wasu da dama suka jikkata kuma ake kula da su a asibitocin.
An fara taron ne da misalin karfe 2:30 na rana, jim kadan bayan dawowar Shugaba Tinubu Abuja daga ziyarar jihohin Plateau, Ogun, Legas da Bayelsa.
A lokacin ziyarar, shugaban ya kaddamar da wasu ayyuka tare da jajanta wa al’ummar jihar Filato kan harin da aka kai a yankin Rukuba.
Manyan shugabannin taron da suka halarta
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da babban hafsan tsaron kasa (CDS), Olufemi Oluyede
Sauran sun hada da Hafsan Sojojin Kasa; Laftanar Janar Waidi Shaibu, Hafsan Sojin Sama; Air Marshal Sunday Anele da Hafsan Rundunar Sojin Ruwa, Vice Admiral Idi Abbas
The Nation ta rahoto cewa Darakta Janar na Hukumar DSS, Oluwatosin Ajayi, shugaban hukumr leken asiri, Mohammed Mohammed da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Olatunji Disu na cikin wadanda suka halarci taron.
Dalilin Tinubu na kiran wannan zama
Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa taron na iya kasancewa yana da alaka da bayanan da shugabannin tsaro suka gabatar dangane da harin kasuwar Jilli.
A halin da ake ciki, fitattun ‘yan Najeriya musamman daga Arewacin kasar sun bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin, yayin da rundunar sojin Najeriya ta fara gudanar da bincike.

Source: Twitter
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce ta kai hare-haren sama kan wuraren ‘yan ta’adda a yankin Jilli na jihar Borno, amma ba ta tabbatar da cewa an kai hari kan fararen hula ba.
Gwamna Zulum ya goyi bayan harin sojoji
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi cikakken bayani game da kasuwar da sojojin sama suka jefa wa bama-bamai.
Gwamna Zulum ya yi ikirarin cewa sun rika sun sanar da rufe kasuwar Jilli shekaru biyar da suka wuce saboda an gano ta zama dandalin ƴan ta'adda.
Ya kuma kara da cewa yana tattaunawa da gwamnatin an jihar Yobe da manyan hafsoshin soji domin fahimtar lamarin da kuma daukar matakan da suka dace.
Asali: Legit.ng
