‘Ka da Ka Roke Shi’: Malami ga Tinubu kan Barazanar Trump, Ya Kawo Masa Mafita

‘Ka da Ka Roke Shi’: Malami ga Tinubu kan Barazanar Trump, Ya Kawo Masa Mafita

  • Malamin addini Kirista, Elijah Ayodele, ya gargadi Bola Tinubu bayan Shugaba Donald Trump ya yi wa Najeriya barazana
  • Fasto Ayodele ya ce ya dade da gargadin Tinubu game da makircin Amurka kan gwamnatinsa da kuma matsalolin tsaro
  • Ayodele ya ce dole ne Tinubu ya magance matsalar tsaro, domin tana iya kawo cikas ga nasararsa a zaben 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele, ya kuma tsoma baki game da barazanar Amurka kan Najeriya.

Fasto Ayodele ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ka da ya nemi zuwa Amurka ko ya roki Donald Trump kan barazanar harin soja da ya yi.

Malami ya gargadi Tinubu kan barazanar Trump
Fasto Elijah Ayodele da Shugaba Donald Trump. Hoto: Primate Elijah Ayodele, Donald J Trump.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a kafafen yada labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar wanda jaridar Tribune ta samu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi halin da Tinubu ke ciki bayan barazanar Donald Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Trump: Gargadin da Fasto ya yi ga Tinubu

Ayodele ya gargadi Tinubu ka da ya sa kansa a matsayin wanda zai dogara da shugaban Amurka, maimakon haka ya dauki mataki cikin gaggawa kan matsalar tsaro saboda tana iya shafar zabensa a 2027.

Malamin ya ce tun shekarun baya ya ke gargadi cewa rashin tsaro zai shafi gwamnatin Tinubu, amma ba a saurare shi ba.

Ya kara da cewa lokaci ya yi da shugaban zai dauki doka a hannunsa ya tunkari lamarin matukar yana so ya kauce wa kalubale mai tsanani.

Ya ce:

“Ka da ya yi tafiya ya je ya roki Trump, shi yana neman kudi ne. Tinubu bai kamata ya nuna kansa a matsayin wanda ke karkashin ikon Trump ba; ya koma ga Allah kuma ya mayar da hankali wajen magance tsaro.
"Na fada tun farko cewa rashin tsaro zai jawo wa gwamnatinsa matsala, kawai ya farka ya tunkari lamarin.”

Kara karanta wannan

'Ba mu tsoronsa': Shin da gaske Tinubu ya furta haka ga Trump? An gano gaskiya

Fasto ya fadawa Tinubu gaskiya kan barazanar Trump
Fasto Elijah Ayodele da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Primte Elijah Ayodele.
Source: Facebook

Fasto ya zargi Trump da manakisa

Ayodele ya bayyana cewa batun Najeriya ya fi abin da Trump ke kiran “kisan kiyashi,” yana mai cewa Amurka tana kokarin amfani da wannan batu ne don cimma muradun tattalin arzikinta.

Ya shawarci Tinubu da ya yi taka-tsantsan wajen karbar shawara daga kasashen waje, domin za a ba shi zabi da ka iya jefa kasa cikin matsala.

“Lamarin Najeriya ya fi abin da ake kira kisan kiyashi. Trump ba abokin Tinubu ba ne tun farko, don haka suna son amfani da wannan lamarin ne don samun dukiyarmu.
"A yi hakuri sosai, domin za su ba shi zabi daban-daban, amma ka da ya dauki wanda zai cutar da kasa.”

Elijah Ayodele

Ya kara da cewa idan gwamnati ta shirya sosai za ta iya warware matsalar ta, yana bayyana cewa Trump ba shi da wata niyya ta gaskiya.

Fasto ya tabbatar da kisan Kiristoci a Najeriya

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ana dar dar a Najeriya, malami ya tabbatar da kisan Kiristoci

Kun ji cewa yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar bayan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi ga Najeriya, Fasto ya goyi bayan zargin kisan Kiristoci.

Donald Trump ya yi barazanar bayan zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci wanda ya tayar da hankula a Najeriya.

Rabaran Ladi Thompson ya soki gwamnatin tarayya, yana cewa akwai kisan kiyashi a Najeriya tun shekaru da dama da suka gabata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.