Harin Amurka: Ana Dar Dar a Najeriya, Malami Ya Tabbatar da Kisan Kiristoci

Harin Amurka: Ana Dar Dar a Najeriya, Malami Ya Tabbatar da Kisan Kiristoci

  • Ana ci gaba da zaman dar-dar bayan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi ga Najeriya saboda rashin tsaro da ke addabar kasar
  • Donald Trump ya yi barazanar bayan zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci wanda ya tayar da hankula a Najeriya
  • Rabaran Ladi Thompson ya soki gwamnatin tarayya, yana cewa akwai kisan kiyashi a Najeriya tun shekaru 20 da suka gabata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fasto kuma masanin tsaro, Rabaran Ladi Thompson, ya yi magana kan barazanar Donald Trump.

Malamin ya kalubalanci ikirarin gwamnatin tarayya cewa babu kisan kiyashi a Najeriya, yana cewa abin yana faruwa.

Malami ya tabbatar akwai kisan Kiristoci a Najeriya
Shugaba Donald Trump da Bola Tinubu. Hoto: Donald J Trump, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

Yayin magana a Channels TV, ya ce kashe-kashen da aka danganta da tsattsauran ra’ayi na addini tsawon shekaru 20 sun isa a kira su kisan kare dangi.

Kara karanta wannan

'Ba mu tsoronsa': Shin da gaske Tinubu ya furta haka ga Trump? An gano gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon hadimin shugaban kasa ya kare Kiristoci

Thompson ya ja hankali cewa rikicin ya kai matakin da zai iya jawo daukar matakin kasashen duniya, yana cewa kasar Amurka ba za ta zuba ido ba.

Faston wanda ya taba zama mai ba wa shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya shawara, ya ce rashin magance tunanin ta’addanci da tsarin da ke goyon bayansa ya kara rikitar da matsalar.

A cewarsa, sama da mutane 200,000 aka kashe cikin shekaru 25 saboda dalilan da ba su dace ba, kuma kowace kasa da ke da shugabanci na gari ya kamata ta magance hakan.

Ya ce tsattsauran ra’ayi ya fara cutar da Kiristoci, musamman fyade da sace yara, daga baya kuma aka fara kashe Musulmai bayan shekaru da dama.

Fasto ya kare maganar kisan Kiristoci a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu yayin jawabi a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Kisan Kiristoci: Ana zargin akwai sakacin gwamnati

Thompson ya kwatanta matsalar da “mai wuyar sha'ani" wanda ya ratsa bangarori kamar siyasa, ilimi, kafofin watsa labarai da sauran muhimman sassa a kasar.

Kara karanta wannan

CAN: Martanin Kiristocin Arewa bisa barazanar Trump na kawo farmaki a Najeriya

Ya ba da misalin wani dan jarida da ya fallasa littafin makaranta mai yada tsattsauran ra’ayi, wanda aka sallame shi, amma daga baya an wanke shi bayan bincike.

Thompson ya ambaci batutuwan Leah Sharibu da Deborah Samuel, yana zargin hukuma da shiru da sakaci, yana cewa hakan mugunta ce ga wadanda abin ya shafa.

Fasto ya caccaki gwamnati kan kisan Kiristoci

A cewarsa duniya tana sane da wuraren ‘yan ta’adda da halin da ake ciki, kuma wasu kasashe ba za su bari Najeriya ta rushe ta jawo barazana ga yammacin Afirka ba.

Ya kuma soki gwamnatin da ta ce babu kisan kiyashi, yana tabbatar da cewa zai ci gaba da bayyana gaskiya don kare rayukan da ke cikin hadari a kasar, cewar Leadership.

Kiristoci sun magantu kan barazanar Amurka

Mun ba ku labarin cewa kungiyar CAN reshen jihohin Arewacin Najeriya ta yi tsokaci kan kalaman shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa ya kamata 'yan Najeriya su yi wa barazanar Trump kallo da idon basira tare da fassara su yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Martanin shugaban sojojin Najeriya kan ikirarin yi wa Kiristoci kisan kare dangi

Barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi na kawo farmaki na ci gaba da daukar hankula bayan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.