'Ba Mu Tsoronsa': Shin da Gaske Tinubu Ya Furta haka ga Trump? An Gano Gaskiya

'Ba Mu Tsoronsa': Shin da Gaske Tinubu Ya Furta haka ga Trump? An Gano Gaskiya

  • An yi ta yada wani faifan bidiyo a kafofin sada zumunta da suka yada inda Bola Tinubu yake martani ga Donald Trump
  • A bidiyon, an ce Tinubu ya ce ba shi da fargaba ga barazanar Trump ko kadan kuma a shirye yake kan haka
  • Al'umma da dama a Najeriya sun danganta hakan da martani bayan barazanar kai hari da Amurka ta yi a kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - A karshen makon da ya gabata ne aka yi ta yada cewa Bola Tinubu ya yi wa Donald Trump martani.

An ce Tinubu ya yi martani ga Trump ne bayan ya yi barazanar daukar matakin soji kan zargin kisan Kiristoci.

An gano gaskiya kan bidiyon Tinubu da ke martani ga Trump
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Donald J Trump, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

A ranar Lahadi 2 ga watan Nuwambar 2025 aka wallafa bidiyon wanda TheCable ta yi binciken kwa-kwaf kan abin da ake yaɗawa.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ana dar dar a Najeriya, malami ya tabbatar da kisan Kiristoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Donald Trump ya ce ga Najeriya

Donald Trump a kwanan nan, ya ayyana Najeriya a matsayin “kasar da ke da matsalar addini”, sannan ya yi barazanar dakatar da tallafi ko tura sojoji.

Maganganun Trump sun jawo tsoro da tattaunawa kan yiwuwar daukar matakin soja daga Amurka kan Najeriya saboda zargin cin zarafin Kiristoci.

A ranar 2 ga Nuwambar 2025 Daniel Bwala ya ce Trump da Tinubu za su gana nan ba da jimawa ba domin tattauna wannan matsala ta zargin kisan Kiristoci.

Babu inda Tinubu ya yi martani ga Trump kan barazanar Amurka a bidiyo
Shugaban kasa, Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Bidiyon da ke yawo a kafofin sadarwa

An wallafa bidiyon da aka gano Tinubu na cewa "ba mu da fargabar abin da Trump ke yi" wanda ya yi yawo a kafofin sadarwa da ya jawo martani tsakanin yan Najeriya.

Wasu masu amfani da Facebook sun danganta wannan magana da kalaman Trump kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya, suna neman a nuna masa wannan bidiyo.

Kara karanta wannan

Martanin shugaban sojojin Najeriya kan ikirarin yi wa Kiristoci kisan kare dangi

Gaskiyar magana kan bidiyon da ake yadawa

Binciken kwa-kwaf ya gano bidiyon tsoho ne daga YouTube, wanda aka dauka ranar 2 ga Satumba 2025 a fadar shugaban kasa.

Bidiyon ya nuna Tinubu na tarbar kungiyar TBO tare da Tanko Al-Makura, inda ya ce tattalin arzikin Najeriya ya inganta da karuwar kudaden shiga.

Tinubu ya ce sun cika burin tara kudin gwamnati kafin karshen shekara, yana cewa harajin cikin gida na tafiya sosai, don haka “babu fargaba ga matakin Trump”.

A lokacin, Trump ya kakaba haraji ga kayayyakin da ake shigo da su daga Najeriya, sannan ya matsa lamba kan OPEC don karin samar da man fetur domin rage farashi.

Gidan talabijin na Arise da Channels TV sun wallafa jawabin Tinubu gaba ɗaya, kuma ya shafi tattalin arziki kawai, ba wani martani ga kalaman da Trump ya yi ba.

Hadimin Tinubu ya kalubalanci Donald Trump

A baya, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kawo hari a Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci.

Kara karanta wannan

An bai wa Tinubu hanyoyin yiwa Trump martani bayan barazana ga Najeriya

Hadimin Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa kuskure ne a dauki irin wannan matakin ba tare da amincewar gwamnati ba.

Daniel Bwala ya kuma musanta zargin cewa ana tsangwamar Kiristoci tare da yi musu kisan gilla a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.