Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Halin da Tinubu Ke ciki bayan Barazanar Donald Trump
- Gwamnatin tarayya ta sake yin magana bayan shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga Najeriya
- Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana cewa shugaban na cikin kwanciyar hankali duk da barazanar farmaki daga Donald Trump
- Hakan na zuwa ne bayan Trump ya yi zargin ana kisan Kiristoci a Najeriya wanda ake ta ƙaryatawa a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta kuma yin martani game da barazanar shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Gwamnatin ta ce hankalin Bola Tinubu a kwance yake duk da barazanar da shugaban Amurka ya yi ga Najeriya.

Source: Twitter
Gwamnatin tarayya ta magantu kan kisan Kiristoci
Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ya tabbatar da haka a yau Talata 4 ga watan Nuwambar 2025, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idris ya ce Shugaba Bola Tinubu yana cikin nutsuwa duk da barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi kan Najeriya.
Ministan ya yi jawabi bayan ganawa da Tinubu a Aso Rock, inda ya ce gwamnati tana daukar matakai na tsaro.
Ya ce Tinubu ya dage wajen tabbatar da cewa Najeriya ta zama kasa mai aminci ga kowa, ko daga wane addini ko kabila, ba tare da wariya ba.
Ministan ya kara da cewa gwamnati tana bayyana wa kasashen duniya irin kokarin da take yi, cewar rahoton Vanguard.
Idris ya tuna cewa Tinubu ya sauya manyan hafsoshin tsaro domin inganta tsaro, kafin Trump ya fara zargin Najeriya.

Source: Facebook
Abin da Tinubu ke yi kan addinai
Ministan ya ce gwamnati ba ta son ta da hankali ko karin rikici a kasar, ya ce an bude hanyoyin tattaunawa da kasashen duniya domin su fahimci abin da Najeriya ke yi da kuma shirinta na gaba.
Game da magance damuwar addinai, Idris ya ce gwamnati na ci gaba da tattaunawa da shugabannin addini, duka Musulmai da Kiristoci.
Ya ce tuni Tinubu ya riga yana ganawa da su domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai inda ya ce zargin cewa gwamnati na goyon bayan kai hari ga mabiya addini ba gaskiya ba ne.
Idris ya ce Najeriya kasa ce mai addinai daban-daban, kuma kundin tsarin mulki ya ba kowa ‘yancin bauta ba tare da tsangwama ba.
Ministan ya ce matsalar Najeriya ta samo asali daga masu tayar da fitina da ‘yan ta’adda da ke kokarin raba kasar.
Idris ya yi kira da a hada kai wajen gina kasa, yana cewa wannan ba lokacin siyasa ko rarrabuwa ba ne, amma lokaci ne na hadin kan kasa, ya ce Tinubu yana kula da lamarin da muhimmanci sosai.
Fasto ya magantu kan kisan Kiristoci a Najeriya
Kun ji cewa yayin da ake cikin fargaba bayan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi ga Najeriya saboda rashin tsaro, Fasto ya fasa kwai.
Donald Trump ya yi barazanar bayan zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci wanda ya tayar da hankula a Najeriya.
Rabaran Ladi Thompson ya soki gwamnatin tarayya, yana cewa akwai kisan kiyashi a Najeriya tun shekaru 20 da suka gabata.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

