Kungiyar Yarbawa Ta Fallasa Shirin Trump kan Shugaba Tinubu

Kungiyar Yarbawa Ta Fallasa Shirin Trump kan Shugaba Tinubu

  • Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta fito ta yi magana kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi wa Najeriya
  • Afenifere ta bayyana cewa barazanar ta nuna yadda Trump ya kullaci Tinubu kan yadda ya ki amincewa da wasu bukatunsa
  • Kungiyar ta kuma yi watsi da zargin da ake ta yadawa na tsangwamar Kiristoci tare da yi musu kisan kiyashi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Kungiyar Afenifete wadda ke wakiltar al’ummar Yarbawa, ta yi martani kan barazanar Donald Trump, ta kawo farmaki a Najeriya domin yakar ‘yan ta’adda.

Kungiyar Afenifere ta ce barazanar wata dabara ce da nufin ɓoye rashin jin daɗin Trump game da matsayar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan wasu batutuwan cikin gida.

Afenifere ta fallasa manufar Trump kan Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Donald Trump Hoto: @OfficialABAT, @WhiteHouse
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Mr. Jare Ajayi, ya fitar a ranar Talata, 4 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Tsohon hafsan sojoji ya gano manufar Amurka kan Najetiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar Afenifere ta ce zargin cewa gwamnatin tarayya tana da hannu a kisan Kiristoci ba shi da tushe, kuma wani yunkuri ne na bata suna don samun hujjar kai hari.

Me Afenifere ta ce kan barazanar Trump?

Hakazalika, kungiyar ta ce akwai dalilai na tattalin arziki da suka sa shugaban Amurka ya dauki irin wannan matsayi.

"Ta hanyar yin barazana, Trump yana son tilasta wa Shugaba Tinubu ya nemi sulhu da shi domin samun karin damar shiga tattalin arzikin Najeriya, musamman wajen sayar da kaya musamman makamai daga Amurka."
"Dangantakar da Najeriya ke kokarin ginawa da kasar China ba ta yi wa Amurka dadi ba."
“Bugu da kari, wasu kungiyoyi a Amurka ba su jin daɗin matakan gwamnatin Bola Tinubu ke dauka kan wasu batutuwa ba.”

- Jare Ajayi

Afenifere ta jaddada cewa Najeriya ƙasa ce mai cikakken ‘yanci, kuma gwamnati ce da alhakin magance matsalar tsaro.

"Gwamnati tana aiki kan batun zaman lafiya ta hannun hukumomin tsaro. Tabbas za a iya kara kokari, kuma sauyin hafsoshin tsaro da shugaban kasa ya yi yana daga cikin matakan da ake dauka don ƙarfafa tsaro."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi halin da Tinubu ke ciki bayan barazanar Donald Trump

- Jare Ajayi

Afenifere ta musanta zargin kisan Kiristoci

Game da zargin kisan gilla ga Kiristoci, Ajayi ya bayyana cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne.

Kungiyar Afenifere ta kare Shugaba Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook
“Ba wai ba a kashe mutane ba ne, amma gaskiyar ita ce ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba sa bambancewa tsakanin addinai."
"Abin da suke nema shi ne tattalin arziki. Wadanda ke daukar nauyinsu suna sha’awar ma’adanai da ke karkashin kasa."
"Suna daukar nauyin ‘yan ta’adda su tayar da tarzoma a yankunan da ke da albarkatu, sannan idan mutane sun gudu, sai su zo su fara tono albarkatun.”

- Jare Ajayi

Dambazau ya fallasa manufar Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hafsan sojojin kasa, Laftana Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya), ya yi tsokaci kan barazanar da Donald Trump ya yi wa Najeriya.

Abdulrahman Dambazau ya bayyana cewa kasar Amurka na son shigowa Najeriya ne domin kafa sansanin sojoji.

Tsohon ministan ya nuna takaicinsa kan yadda wasu 'yan Najeriya ke nuna goyon bayansu ga karyar da wasu 'yan kasashen waje ke yadawa kan zargin kisan Kiristoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng