Burna Boy: Yadda Fitaccen Mawakin Najeriya Ya Gano Musulunci ne Gaskiya

Burna Boy: Yadda Fitaccen Mawakin Najeriya Ya Gano Musulunci ne Gaskiya

  • Fitaccen mawaki Burna Boy da ya musulunta ya bayyana yadda ya ya samu kansa a Musulunci bayan zama Kirista
  • Ya bayyana cewa duk da bincikensa game da addinai daban-daban, hakan ya kara masa rudani game da rayuwa
  • Burna Boy ya kuma bayyana cewa ya taso cikin addinin Kirista ne saboda haka iyayensa suka yi imani da shi a karon farko

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Mawakin Najeriya da ya lashe lambar yabo ta Grammy, Damini Ogulu wanda aka fi sani da Burna Boy, ya bayyana dalilin da ya sa ya musulunta.

Burna Boy ya ce sauya addininsa daga Kiristanci zuwa Musulunci wani ɓangare ne na neman fahimtar gaskiyar rayuwa da natsuwar zuciya.

Burna Boy
Burna Boy yana zaune a wani waje. Hoto: Burna Boy
Source: Facebook

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da mai watsa shirye-shirye, Playboymax, inda ya ce duk da zurfafa bincikensa cikin addinai, hakan bai ba shi cikakkiyar amsar da yake nema ba.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ana dar dar a Najeriya, malami ya tabbatar da kisan Kiristoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Burna Boy ya Musulunta bayan bincike

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yayin da ya ke bayar da labarin yadda ya Musulunta, Burna Boy ya ce:

“Na taso a matsayin Kirista sannan daga baya na musulunta. Na yi nazari kan dukkan addinai, amma na cigaba da neman gano gaskiya, ka gane? Maimakon samun amsa, sai na kara rikicewa.”

Burna Boy ya bayyana cewa bincikensa ya haifar masa da tambayoyi masu zurfi game da makomar addini da rayuwa.

Tarihin rayuwar mawaki Burna Boy

An haifi Burna Boy a birnin Port Harcourt, Najeriya, a ranar 2, Yuli, 1991, iyayensa kuma su ne Bosede da Samuel Ogulu. Shi ne ɗa namiji kaɗai kuma babba a cikin ‘ya’yansu uku.

Ya fara shirya kiɗa tun yana da shekara 10, kafin daga bisani ya tafi Landan don yin karatu bayan kammala sakandare.

Burna Boy
Burna Boy yayin rera wata waka. Hoto: Burna Boy
Source: Facebook

Shafin Universal Music ya wallafa cewa bayan shekara biyu a jami’a, sai ya bar karatun don komawa Najeriya ya ci gaba da sana’ar waka.

Kara karanta wannan

Martanin shugaban sojojin Najeriya kan ikirarin yi wa Kiristoci kisan kare dangi

Mawakin ya yi karatu a makarantar Montessori International da ke Port Harcourt daga 1993 zuwa 2002, sannan ya tafi Sakandare ta Corona da ke Legas daga 2002 zuwa 2008.

Tarihin da Burna Boy ya kafa a Amurka

Bayan lashe zaben da tsohon shugaban Amurka, Joe Biden ya yi, an sanya wakar Burna Boy ta Destiny a wajen taron rantsar da shugaban kasa.

Legit Hausa ta rahoto cewa Burna Boy ne dan Afrika tilo da aka saka wakarsa a taron rantsar da shugaba Joy Biden da Kamala Harris.

Zakzaki: Malamin Musulunci ya soki Trump

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Ibrahim Zakzaky ya yi magana kan zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi da Donald Trump ya yi.

Malamin ya bayyana cewa babu wani dalili da ya ke nuna cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Zakzaky ya yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da hada kai domin magance matsalolin da suka addabi kasar baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng