Biden: ‘Destiny’ ta samu shiga cikin jerin wakokin da za a saurara wajen rantsarwa

Biden: ‘Destiny’ ta samu shiga cikin jerin wakokin da za a saurara wajen rantsarwa

- Wakar Burna Boy za ta tashi a bikin rantsar da Joe Biden da Kamala Harris

- Wadanda su ka tsara bikin da za ayi sun zabi wakar Destiny da aka yi a 2019

- Burna Boy ne kadai Tauraro daga kasar Afrika da za a saurari wakarsa a yau

Fitacciyar wakar nan ta ‘Destiny’ da Burna Boy ya rera ta na cikin wakokin da za a saurara a wajen bikin rantsar da sabon shugaban kasar Amurka.

A yau Laraba, 20 ga watan Junairu, 2021, za a rantsar da Joe Biden da kuma Kamala Harris a matsayin shugaban kasa da mataimakiyarsa a Amurka.

Wakar ‘Destiny’ wanda ita ce ta 13 a kundin da Burna Boy ya fitar a 2019 ta samu shiga a wannan gagarumin taro da za a yi a babban birnin Washington DC.

Premium Times ta fitar da wannan rahoto, ta ce Burna Boy ne kadai mawakin daga nahiyar Afrika wanda wakarsa za ta tashi wajen bikin rantsarwar.

KU KARANTA: Ba mu jefa Amurka a yaki ba - Mataimakin shugaban Kasar Amurka, Pence

Shugaban kwamitin rantsar da sabon shugaban kasar Amurka, Tony Allen, ya bayyana dalilinsu na zaben wannan shahararriyar waka ta Burna Boy.

The Insider ta rahoto Mista Tony Allen yana cewa sun zabi wannan waka ta ‘Destiny’ ne saboda irin bayanan da mawakin Najeriyar ya kunsa a cikinta.

A cewar Allen, Burna Boy ya bayyana arziki da kishin irin na Amurka a cikin wakar da ya rera a 2019.

Wadanda suka shirya wannan biki sun ce wakokin da aka zaba za a ji yau, za su taimaka wajen bude sabon shafi a Amurka a karkashin jagorancin Joe Biden.

KU KARANTA: Tarihin Matar da ta tsige Shugaba Donald Trump sau biyu

Biden: ‘Destiny’ ta samu shiga cikin jerin wakokin da za a saurara wajen rantsarwa
Mawaki Burna Boy Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sauran mawakan da za su yi wasa a wajen sun hada da irinsu Lady Gaga wanda za ta rera taken Amurka, haka zalika Jennifer Lopez za ta rera wasu wakokinta.

Dazu kun ji labari cewa yayin da shugaban Amurka, Joe Biden mai jiran-gado ya isa Washington, Donald Trump ya yi gaba, ya tattara ya bar fadar White House.

A halin yanzu, saura kiris a rantsar da Joe Biden da Kamala Haris a kan kujerar mulki.

Ana sa ran cewa Donald Trump zai yi wa wasu mutane afuwa kafin ya sauka daga kan kujera. Daga cikinsu watakila akwai tsohon hadiminsa, Steve Bannon.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel