Buhari, Atiku, PDP da APC sun taya Wiz Kid da Burna Boy lashe kyaututtukan waka

Buhari, Atiku, PDP da APC sun taya Wiz Kid da Burna Boy lashe kyaututtukan waka

- Wizkid da Burna Boy su na cikin wadanda su ka lashe kyautar Grammy

- Mawakan Najeriyar sun sa kasarsu Najeriya alfahari da wannan nasara

- Atiku Abubakar da su Bukola Saraki sun taya manyan mawakan murna

Ayo Balogun wanda aka fi sani da Wizkid, da Burna Boy sun ci kasuwar kyaututtukan waka na Grammy da aka bada a ranar 14 ga watan Maris, 2021.

Manyan taurarin Najeriya sun jawo wa kasarsu abin alfahari da wannan babbar nasara da su ka samu.

Wizkid ya samu kyautar Grammy na farko bayan wakarsa ta ‘Brown Skin Girl’ da wakar da su ka yi tare da shahararriyar mawakiya Beyonce sun yi zarra.

Bidiyon wakar da ta fi kowace kyau ita ce 'BROWN SKIN GIRL’ wanda taurariyar Amurka Beyonce ta shirya tare da matashin mawaki Wiz Kid da Blue IVY.

Shi kuma Burna Boy ya lashe kyauta ne da kundin wakokinsa na ‘TWICE AS TALL’. Mawakin ya doke Antibalas, Bebel Gilberto, Anoushka Shankar da wasunsu.

KU KARANTA: Mai dakina Chioma ta kamu da coronavirus - Davido

Sau biyu kenan a jere Burna Boy ya na samun kyauta a wajen bikin Grammy wanda shi ne babban taron mawaka da BET ta ke shirya wa a kowace shekara.

Wadanda su ka fito su ka taya Burna Boy, Wizkid, Tiwa Savage, da kuma Femi Kuti murna sun hada da Atiku Abubakar, Ben Murray Bruce, da Bukola Saraki.

Atiku Abubakar ya rubuta: “Congrats @BurnaBoy! #Grammys," ya ce nasarar ta sa shi alfahari.

Bukola Saraki ya ce: “Ina taya ku murna @Burnaboy da @Wizkidayo! #GRAMMYs #NigeriaToTheWorld”

Atiku, Sanatoci, da Davido sun taya Wiz Kid da Burna Boy lashe kyaututtukan waka
Wiz Kid da Burna Boy
Asali: Instagram

KU KARANTA: An yi cacar baki tsakanin Wizkid da hadimar Shugaban Najeriya

Ben Murray-Bruce ya rubuta a shafinsa na Twitter: “Congrats, Burna, da ka kawo kyautar #GRAMMYs gida. Ina alfahari da zama ‘dan Najeriya. @burnaboy”

Shehu Sani ma ya taya taurarin; @burnaboy da @wizkidayo murnar lashe wadannan kyatuttuka.

Davido wanda shi ma mawaki ne ya ce ko ta ya aka duba lamarin, Najeriya ce ta yi nasara, ko da bai ambaci sunaye ba, ya taya mawakan kasar murnar wannan nasara.

Gwamnatin Najerita ta taya wadannan taurari murnar samun wannan kyauta. Sakon taya murnar ya fito ne ta bakin Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed.

Ministan ya yi magana ta bakin Hadiminsa, Mr. Segun Adeyemi, a ranar Litinin da rama. Ministan ya ce Burna Boy da Wiz Kid sun cancanci su lashe kyaututtukan.

Haka zalika manyan jam'iyyun PDP da APC duk sun aika wa taurarin sakon taya murna.

Kwanakin baya aka ji cewa Mawaki Ayodeji Balogun wanda aka fi sani da Wizkid ya yi magana a kan kokarin majalisar Najeriya na haramta shigo da injin samar da wuta.

Shirin haramta shigo da janareto cikin kasar nan domin samar da wutar lantarki.

arki da majalisar dattawa ta yi yunkurin yi ya jawo wa Sanatocin sukar irinsu Wiz Kid.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng