Sabon Rikici Ya Barke a Wani Yankin Kaduna, An Kashe Fiye da Mutane 5 a Rana 1

Sabon Rikici Ya Barke a Wani Yankin Kaduna, An Kashe Fiye da Mutane 5 a Rana 1

  • Wani sabon rikici ya barke tsakanin masu hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba da ‘yan bindiga a karamar hukumar Birnin Gwari
  • Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne bayan an kashe wani dan bindiga da ya nemi haraji daga wajen masu hako ma’adanan
  • Duk da cewa rundunar 'yan sanda ba ta fitar da rahoto a hukumance ba, amma an ji matakin da jami'an tsaro suka dauka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - An samu mummunan rikici tsakanin wasu masu hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma ‘yan bindiga a jihar Kaduna.

An rahoto cewa rikicin ya faru ne a yankin Kuyello, karamar hukumar Birnin Gwari, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane bakwai.

'Yan bindiga da masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba sun gwabza fada a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mazauna yankin sun shaidawa Channels TV cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar a ranar Alhamis, 16 ga Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Kwarton da miji ya lakadawa duka ya mutu kan shiga wajen matarsa da dare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya jawo rikici a Kaduna

Wani shugaban al’umma a yankin, Umar Maishanu, ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan wani dan bindiga da ya fito daga Zamfara ya nemi kuɗin haraji daga wajen masu hakar ma’adinai.

Maishanu ya ce masu hakar ma’adanan sun ki amincewa da biyan kuɗin, inda suka yi fada da dan bindigar har suka kashe shi, suka kuma birne gawarsa a rami mai zurfi.

Wannan mataki, a cewarsa, ya fusata abokan aikin mamacin, wanda hakan ya sa suka yo zuga, suka kaddamar da harin ramuwar gayya kan masu hakar ma’adanan.

A lokacin farmakin, an kashe mutane bakwai ciki har da wasu daga cikin masu hakar ma’adinai, yayin da wasu suka tsere cikin daji don tsira da rayuwarsu.

Kaduna: An tura jami'an tsaro Kuyello

Duk da cewa hukumar ‘yan sanda ba ta fitar da sanarwa ba tukuna, amma wata majiya ta tabbatar cewa an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin hana karin rikici.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun lallaba cikin masallaci ana sallar asuba, sun sace mutane

Majiyar ta kara da cewa an kama wasu daga cikin ‘yan bindigar da suka yi yunkurin tserewa zuwa jihar Zamfara bayan artabun.

Rahotanni sun nuna cewa an jima ba a samu tashin hankali a yankin Birnin Gwari kamar irin na wannan lokaci ba, tun bayan kokarin gwamnati wajen samar da zaman lafiya a 2024.

An ruwaito cewa an tura jami'an tsaro domin kwantar da tarzoma a yankunan Kaduna
Hoton wasu daga cikin motoci da gwamnati ta ba 'yan sandan Kaduna don inganta tsaro. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

An bukaci a haramta hakar ma’adanai

Biyo bayan wannan rikicin, mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta hana hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Sun bayyana cewa wadannan wurare sun zama mafakar masu laifi da ke amfani da hakar a’adinai wajen samun kudin sayen makamai.

A makon nan ne Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba na barazana ga zaman lafiya da ci gaban yankin yammacin Afirka.

Ramin hakar ma'adanai ya rufta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mummunan ibtila'i ya ritsa da wasu mutanen da suka fita zuwa wajen aikin hakar ma'adanai a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Baya ta haihu: Akwai yiwuwar Tinubu ya janye afuwa ga wasu 'yan Najeriya

An ce wani ramin hakar ma'adanai ya rufta kan ma'aikata a lokacin da suke baki aiki a karamar hukumar Maru, wanda hakan ya jawo asarar rayuka.

Majiyoyi sun bayyana cewa akwai sama da mutane 100 a cikin ramin hakar ma'adanan lokacin da ya rufta musu, amma ba duka ne suka mutu ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com