Rami ya rufta da masu hakar ma'adanai, 3 sun mutu, da dama sun jikkata

Rami ya rufta da masu hakar ma'adanai, 3 sun mutu, da dama sun jikkata

  • A jihar Benue, wasu mahaka ma'adanai sun hallaka yayin da suke tsaka da aiki a cikin rami
  • Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Talata 28 ga watan Satumba
  • Shugaban karamar hukumar yankin da lamarin ya faru ya bayyana gaskiyar yadda lamarin ya faru

Benue - Mutane uku sun mutu bayan da wata mahakar ma'adanai da suke aiki a ciki ta rufta a yankin Anyiin da ke karamar hukumar Logo a jihar Benue, ranar Talata 28 ga watan Satumba.

Wakilin Daily Trust ya tattaro cewa marigayan sun kasance suna cikin hako ne lokacin da ramin ya rufta dasu.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce mamatan sun mutu nan take yayin da mutanen gari kuwa suka yi kokarin ceto wadanda suka jikkata.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Shaidu sun ce wasu kalilan da suka jikkata an kai su asibiti nan da nan don duba lafiyarsu.

Rami ya rufta da masu hakar ma'adanai, 3 sun mutu, da dama sun jikkata
Taswirar jihar Benue | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da aka tuntube shi, shugaban karamar hukumar Logo, Kwamared Terseer Agber, ya ce duk da bai san da masu hakar ma'adinan a yankinsa ba, kamfanin, duk da haka, ya shigo da takardunsa (wai daga gwamnatin tarayya) kuma sarakunan yankin sun ba shi izinin aiki.

Agber ya ce:

"Da sanyin safiyar yau (Talata), aka kira ni aka sanar da ni cewa kimanin mutane hudu sun makale a ramin hakar ma’adinai. Don haka na ba da umarni cewa a yi kokari a yi wani abu kuma daga baya sun dawo sun ba da rahoton cewa sun gano gawarwaki uku da guda daya da ya jikkata.
"Na sha kiran a yi taro tare da su don warware lamarin, amma duk da haka taro ya gagara. Gwamnatin jihar na sane da ayyukan su a yankin.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

“Gwamna Samuel Ortom ya tura Kwamishinoni guda biyu ciki har da na Noma; Filaye, Bincike da Ma'adanai masu karfi, amma babu abin da ya faru.
"Masu hakar ma'adinan sun ce ba su da wata alaka da gwamnatin jihar, cewa sun samo lasisin su ne daga Abuja kuma dama hakki ne na Gwamnatin Tarayya, ba su da wata alaka da gwamnatin jihar Benue."

A halin da ake ciki, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Benue, DSP Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu wani bayani game da lamarin ba.

'Yan bindigan Zamfara: Mun haramta hakar ma'adinai a yankunan da muke aiki

Watannin da suka gabata, wani shugaban ‘yan bindiga a jihar Zamfara, Shehu Rekeb, ya ce kungiyar sa ta haramta ayyukan hakar ma’adanai a duk wuraren da su ke aiki.

Gwamnatin Tarayya ta alakanta ayyukan masu hakar ma'adanai da 'yan bindiga, kuma ta ba da umarnin dakatar da hakar ma'adanai a jihar.

Kara karanta wannan

Mutane 13 sun mutu a hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, ciki har da ƙanin ango da matarsa

Amma a zantawarsa da Daily Trust, Rekeb ya ce tun kafin umarnin na gwamnatin tarayya, kungiyar tasa ba ta barin masu hakar ma’adanai a wuraren da suke da karfi.

A cewarsa:

“A da, fararen fata su kan tafi mahakar ma'adinai tare da rakiyar jami'an tsaro amma yanzu an daina hakan.
“Mun hana… amma makiyaya ba su san yadda ake hakar ma'adinai ba. Mutanen da muke bai wa izini su ne kauyukan da suke talakawa kuma ba su da abinda zasu rayu dashi.
"Muna ba su damar shiga wasu wurare don samun abin da za su rayu da shi. Amma mun hana hakar ma’adanai."

Gwamnatin Buhari ta fara bin coci don yiwa masu bautar ranar Lahadi riga-kafin Korona

A wani labarin, Gwamnatin tarayya a ranar Talata 14 ga watan Satumba ta sanar da shirinta na daukar allurar riga-kafin Korona zuwa cibiyoyin bauta ta Kiristoci, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta

Babban Darakta na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib, ya bayyana hakan ne yayin wayar da kan shugabannin Kiristoci kan kashi na biyu na riga-kafin Korona a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce:

“Mai martaba, Shugaban CAN, fitattun shugabannin Kirista, mata da maza, ina mai farin cikin sanar da ku cewa daga wannan mataki na 2 na riga-kafin Korona, mun gabatar da allurar riga-kafin ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.