Baya Ta Haihu: Akwai Yiwuwar Tinubu Ya Janye Afuwa ga Wasu 'Yan Najeriya

Baya Ta Haihu: Akwai Yiwuwar Tinubu Ya Janye Afuwa ga Wasu 'Yan Najeriya

  • Majalisar Dattawa da sauran hukumomin tsaro na duba yiwuwar cire wasu sunaye daga jerin wadanda aka yafe wa laifi a Najeriya
  • Wannan ya biyo bayan suka daga jama’a game da yafe wa manyan masu laifi da suka hada da masu kisan kai da safarar kwayoyi
  • Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya ce ba a fitar da takardar saki ga kowa ba tukuna, domin ana sake nazarin wadanda aka yafewa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai yiwuwar a cire wasu sunaye daga jerin wadanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa.

Sake nazarin wadanda aka yi wa afuwa ya biyo bayan korafe-korafe da suka biyo yafe wa wasu daga cikin mutane 175 a kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan shan suka, gwamnatin Tinubu ta yi magana kan sakin Maryam Sanda da sauran masu laifi

Shugaban kasa zai iya janye afuwa da wasu 'yan Najeriya
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta wallafa cewa Shugaba Tinubu ya yafe wa mutanen ne bayan amincewar Majalisar Koli ta Kasa.

Daga cikin wadanda aka yafe wa akwai a tsofaffin sojoji, ‘yan kasuwa, lauyoyi da masu laifi masu nasaba da kisan kai, rashawa da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Afuwar Tinubu ta jawo cece-kuce

Wasu daga cikin wadanda suka janyo cece-kuce a jerin wadanda Tinubu ya yafe wa sun hada da Maryam Sanda.

Kotu ta yanke wa Maryam hukuncin kisa ne bayan an kama ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello a 2017.

Yafe wa Maryam Sanda ya jawo cece-kuce
Bilyaminu Bello, Maryam Sanda da Shugaba Tinubu Hoto: Dada Olusegun
Source: Facebook

Sai kuma Kelvin Oniarah, wanda ya yi kaurin suna a garkuwa da mutane a jihohin Kudu da Arewa ta Tsakiya.

A wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, an bayyana cewa jerin sunayen an rarraba shi zuwa rukuni shida da suka hada da yafe laifuffukan baki daya.

Sannan an yafe wa wadanda su ka rasu, girmamawa ga wadanda suka rasa rayukansu, sassauta hukunci, da kuma sauya hukuncin kisa zuwa dauri na rai da rai.

Kara karanta wannan

Farouk Lawan: Tsohon 'dan majalisa ya rabu da Kwankwasiyya bayan barin kurkuku

Ana nazarain afuwar Tinubu

Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, ya ce har yanzu ana nazarin sunayen, kuma babu wanda aka saki daga gidan yari tukuna.

Ya ce dole ne a tabbatar da cewa duk sunayen sun cika ka’idar doka kafin a fitar da takardar sakinsu daga gidan yari domin su shaki iskar ‘yanci.

Hukumomin EFCC, ICPC, da NDLEA sun nuna damuwa kan sunayen da suka bayyana a jerin sunayen da aka ce sun samu afauwar Tinubu.

Sannan hukumomin sun yi zargin cewa sunayen ba su fito daga daga kwamitin da ya tantance sauran wadanda aka yi wa afuwa ba.

Haka kuma, ana zargin wasu ma’aikata ne su ka sanya sunayen ta bayan fage domin mutanensu su samu fito wa daga gidan yari.

Wani jami’in tsaro ya ce:

“Wasu daga cikin wadanda ke cikin jerin ba za a taba sakinsu ba saboda suna da hannu a kisan jami’an tsaro ko garkuwa da mutane.”

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

Fagbemi ya gode wa jama’a bisa kulawa da korafe-korafen da aka gabatar, yana mai cewa hakan alama ce ta damuwa da adalci.

An yi tir da afuwar gwamnatin Tinubu

A baya, mun wallafa cewa 'yan uwan marigayi Bilyaminu Bello sun fitar da sanarwa inda suka soki matakin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na yafe wa Maryam Sanda.

Sanarwar, wacce Dr. Bello Mohammed ya fitar a madadin 'yan uwan, ta bayyana cewa wannan yafiya babban zalunci ce ga adalci kuma ya dawo masu da ciwon rasa 'dansu danye.

A cewarsu, Maryam ta ki nuna nadama tun bayan aikata laifin, kuma tafiyar ta nuna cewa ana son dadadawa dangin Maryam a maimakon tabbatar an yi adalci gare su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng