'Na Yiwa Ƴan Izalah Ma Fim': Tijjani Faraga Ya Yi Martani ga Sheikh kan Kalamansa
- Jarumin Kannywood, Tijjani Faraga ya mayar da martani ga caccakar da shehin malami ya masa bayan ya bayyana cewa shi ɗan Tijjaniya ne
- Malamin ya ce Izalah ba ta alfahari da irin Faraga, yana zarginsa da shiga ayyukan da suka sabawa tafarkin Ahlus Sunnah wal Jama’a
- Faraga ya ce ya taba yin aiki da Izalah kuma ya ba da gudunmawa, don haka bai cancanci cin mutunci ba saboda bayyana matsayinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jarumin Kannywood, Tijjani Faraga ya yi magana bayan shehin malami da ya caccake shi kan akidarsa.
Ana zargin Faraga ya yi martani ne kan maganganun Sheikh Abubakar Lawan Triumph game da barranta kansa da Izalah.

Asali: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da jarumin ya wallafa a shafin Facebook a jiya Asabar 5 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya jawo cece-kuce game da Faraga
Hakan ya biyo bayan caccakar Faraga da malamin ya yi bayan jarumin ya ce shi ɗan darikar Tijjaniya ne.
Martanin jarumin ya biyo bayan zargin ana amfani da manhajarsa a kafofin sadarwa wurin danganta shi da Izalah.
A bidiyon ya ce shi ɗan darikar Tijjaniyya ne cikakke kuma bai yin nadamar haka.
Wannan kalamai na shi ya ta da kura inda mutane da dama suka dura kansa game da barranta kansa da Izalah.
Shi ma Sheikh Triumph ya yi magana a wani bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.
Malamin cikin fushi ya ce ai dama izalah ba ta alfahari da irinsu saboda ahlul sunnah ba su shiga ayyukan badala.

Asali: Facebook
Martanin Tijjani Faraga ga malamin Izalah
Daga bisani, Faraga ya nuna bacin ransa game da kalaman malamin inda ya ce ko ba komai ya yi wa Izalah rana.
Ya ce:
"Abin da zan fada maka a nan, ka bude manhajar YouTube ka rubuta iyalina za ga ka fim da na yi wa Izalah mai dogon zango.
"Ana nuna shi tun ranar da aka fara azumi har zuwa jajiberi, mun yi iyalina ya yi nasara, a shekarar na sha godiya daga gare su.
"Da kansu suka sake nemo ni da shekara ta yi, muka zo muka zauna muka fitar da labari har na ba su shawara ku tafi Jigawa.
"Ashe ko, ko dalilin gudunmawar da na bayar ya kamata a yi min uzuri, laifi na shi ne don na nuna fushi da barranta kaina da izalah? Ai ba zagi na yi ba kuma ban ci mutuncin kowa ba."
Fim a idon malaman Izala
Musanyar miyau tsakanin wasu malamai na kungiyar Izala da jaruman Kannywood kamar Tijjani Faraga ba sabon abu ba ne.
Izala na daga cikin kungiyoyin addini da ke da tsayayyen matsayi kan fina-finan Hausa da masana'antar Kannywood gaba ɗaya.
Ga yawancin mambobinta, Kannywood tana wakiltar al'ada da salon rayuwa da ke karya tarbiyya da janyo sabawa addini, musamman ma a cikin matasa.
Izala tana kallon fina-finai na Husa a matsayin wata hanya da ke kawo fitina, cin mutunci, da kuma yada iskanci da halaye marasa kyau a cikin al’umma.
A ganinsu, jaruman Kannywood ba su cika bin dokokin addini ba, musamman ta fuskar sutura, hulɗa tsakanin maza da mata, da kuma abinda ke gudana a cikin fina-finansu.
Saboda haka, duk wani ɗan fim da ya nuna alaka da Izala ko ya tsaya da wata fahimta daban – kamar yadda Faraga ya bayyana kan akidar Tijjaniyya – yana fuskantar suka daga mambobin kungiyar.
Wannan ya sa ake ganin cewa zargin da Sheikh Abubakar Lawan Triumph ya yi wa Faraga ba kawai yana kan akida ba ne, har ila yau yana cikin dogon rikicin tsakanin al’ada da addini a arewacin Najeriya, inda fina-finai da dariku ke ci gaba da jefa mutane biyu cikin rikici.
Dantata: Sheikh ya caccaki tawagar Sanusi II
A baya, mun ba ku labarin cewa Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph ya nuna takaici kan cin mutuncin da aka yi wa Alhaji Aminu Dantata a lokacin bukukuwan Sallah a Kano.
A cikin hudubarsa ta Juma'a, Sheikh Triumph ya soki wasu daga cikin tawagar Sarki Sanusi II da suka zagi dattijon attajirin, har suna buga bindiga.
Malamin ya bayyana Dantata a matsayin dattijo da tarihin Kano ba zai cika ba tare da ambatonsa, yana kiran al'umma da su mutunta dattijai.
Asali: Legit.ng