‘Zan Dawo 'Dan Bindiga ko Boko Haram’: Matashi Ya Yi Barazana, Ya ba da Wa’adi

‘Zan Dawo 'Dan Bindiga ko Boko Haram’: Matashi Ya Yi Barazana, Ya ba da Wa’adi

  • Wani matashi ya yi barazanar shiga Boko Haram ko masu garkuwa da mutane idan ba ta ba shi jari ko kuma aikin yi ba
  • Matashin ya bayyana fushinsa a bidiyo da aka wallafa, yana cewa talauci ya fi ciwo kuma ya gaji da zama a wannan hali
  • Ya ce idan har bai samu taimako kafin Laraba mai zuwa ba, zai shiga ta'addanci, ya kuma kalubalanci masu kiransa mahaukaci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Yayin da lamura ke sake dagulewa a Najeriya, wani matashi ya yi bidiyo inda yake barazana kan halin da ya shiga.

An gano matashin da ba a bayyana sunansa ba amma kamar daga Maiduguri yake yana barazanar shiga Boko Haram ko kuma cikin masu garkuwa da mutane.

Matashi ya yi barazanar shiga ta'addanci a Najeriya
Wani matashi daga Borno ya yi barazanar shiga Boko Haram kan wasu bukatu. Hoto: HQ Nigerian Army, @zagazOlamakam.
Asali: Twitter

Bidiyon matashi na barazanar shiga Boko Haram

Shafin Zagazola Makama shi ya wallafa faifan bidiyon matashin a daren jiya Alhamis 3 ga watan Yulin 2025 a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, an gano matashin ya na cewa idan har ba a biya masa bukatunsa ba kan halin da ya shiga komai zai iya faruwa.

Matashin a cikin maganganunsa ya yi ta kunno ashariya wanda ya tabbatar da cewa yana cikin fushi kuma zai iya yin komai.

Ya ce idan har ba a ba shi jari ba ko kuma mayar da shi wurin aikinsa zai shiga Boko Haram ko kuma cikin masu garkuwa da mutane.

Ya ce:

""Magana daga bakin mai ita, an ce baki shi ke yanka wuya, ta yanka ciki ma.....
"Na dawo ne yanzu zan yi magana in ba da sharadi da kuma korafi, billahillazi la ilaha illa huwa idan ba a taimake ni ba da jari ko mayar da ni aiki ba sai na shiga Boko Haram.

"Ko kuma na shiga cikin yan ta'adda masu garkuwa da mutane idan ba haka ba Allah ya tsine mani albarka, wallahi tallahi."
Wani matashi ya bukaci taimakonsa ko ya shiga Boko Haram
Fusataccen matashi ya yi barazanar shiga Boko Haram. Hoto: Legit.
Asali: Original

Wa'adin da matashin ya bayar a Borno

Matashin ya caccaki masu cewa ya haukace inda ya ce a yanzu babu ciwo ko haukar da ta fi talauci.

Har ila yau, ya ba da wa'adin mako daya zuwa ranar Laraba mai zuwa idan ba a taimake shi ba zai iya shiga ta'addanci.

Ya kara da cewa:

"Idan kuma ka ce na haukace ne, kai ni asibitin mahaukata na Maiduguri, ba a taimake ni ba, akwai ciwon da ya fi talauci ne.
"Wallahi tallahi na ba da daga nan zuwa sati mai zuwa ranar Laraba idan ba sai na fada Boko Haram ba Allah ya tsine mani."

Matashin ya yi ta yin ashariya ga mutane da ba su taimake shi ba inda ya ke sukar masu ce masa ya haukace ne.

Legit Hausa ta tattauna da wani matashi

Dan gwagwarmaya, Sani Aluta ya ce irin wadannan matasa fa suna da yawa a Najeriya kawai ba su fito sun yi bayani ba ne.

Ya ce:

"Ana cikin mummunan yanayi a Najeriya, wannan shi ya bayyana kansa ne ma amma akwai dubbansu a boye."

Sai dai Kwamred din ya ce hakan ba shi ne mafita ba ko a addini hakan bai kamata ba.

Ya bukaci matasa su tashi tsaye domin dogaro da kansu saboda gudun shiga irin wannan yanayi.

Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram

Kn ji cewa sojojin Najeriya sun kashe wasu daga cikin mayakan ISWAP da suka yi yunkurin dasa bama-bamai a hanyar Trans-Timbuktu, jihar Borno.

Majiyoyin tsaro ta bayyana cewa sai da aka fafata da yan bindigar, inda bayan sun ji ruwan wuta, wasu daga cikinsu suka tsere.

An kwato bindigu AK-47, babur, da kayan hada bama-bamai, tare da kayan da ake amfani da su wajen huda hanya domin boye bama-bamaI.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.