Natasha Vs Akpabio: Kotu Ta Gano Mai Laifi, Ta Yanke Hukunci kan Dakatarwar Watanni 6
- Kotun Tarayya mai zama a Abuja ya ci tarar Sanata Mai Wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan N5m kan laifin raina umarninta
- Mai Shari'a Binta Nyako ta ce sakon ba da haƙuri na wulaƙanci da Natasha ta wallafa a shafinta ya saɓawa umarnin da kotu ta bayar
- Bayan haka kotun ta umarci Majalisar Dattawan Najeriya ta dawo da Sanata Natasha kan kujerarta, tana mai cewa dakatarwar wata shida ta yi yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta kama Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da laifin raina umarnin da ta bayar a baya.
A zamanta na yau Juma'a, 4 ga watan Yuli, 2025, kotun ta bayyana cewa ta gamsu Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta aikata laifin raini ga kotu, ta ci tararta N5m.

Asali: Facebook
Kotun ta kuma umarci Majalisar Dattawa Najeriya ta maida dakatacciyar Sanatar kan kujerarta, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta gamsu Sanata Natasha ta yi laifi
Mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ce ta yanke wannan hukunci a yau Juma'a.
Ta ce Sanata Natasha ta karya umarnin kotun ta hanyar wallafa saƙon neman afuwar shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, cewar Vanguard.
Ta ce sakon ba da haƙurin, wanda Natasha ta saki a shafinta na Facebook ranar 7 ga watan Afrilu, 2025, ya saɓa umarnin hana kowane ɓangare magana kan batun da ke gaban kotu.
Kotu ta hukunta Sanatar Kogi ta Tsakiya
Da take yanke hukunci kan laifin raina kotu, Mai Shari'a Binta Nyako ta umarci Natasha ta bada haƙuri a manyan jaridu biyu na ƙasa, kuma ta wallafa a shafinta na Facebook cikin mako guda.
Haka kuma, kotun ta umarci sanatar biya tarar Naira miliyan biyar (₦5m) bisa laifin da ta aikata na raina ta.
Duk da cewa hukuncin ya fito ne daga ƙarar raina kotu da Sanata Akpabio ya shigar, kotun ta ƙi cewa komai kan wannan batu na shugaban Majalisa.

Asali: Twitter
Kotu ta umarci a dawo da Natasha bakin aiki
Babbar Kotun ta kuma bayar da umarni cewa a janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.
Mai Shari’a Binta Nyako ta bayyana cewa dakatarwar wata shida da Majalisar Dattawa ta yi wa Sanata Akpoti-Uduaghan “ta yi tsanani sosai”.
Mai shari’a Nyako ta soki wasu tanade-tanade da ke cikin Sashe na 8 na Dokokin kafa Majalisar Dattawa da kuma Sashe na 14 na Dokar Ƙarfafa Ikon Majalisar Dokoki.
Yadda aka gurfanar da Natasha a kotu
A wani rahoton, kun ji cewa tun farko an gurfanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, a gaban kotu.
Masu ƙara na zargin Sanata Natasha ta ɓata sunan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
A yayin da aka karanta mata tuhume-tuhumen da ake yi mata, Sanata Natasha ta musanta aikaya dukkansu nan take.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng