INEC Ta Samu Karin Kungiyoyi 12 da ke Neman Rajistar Jam'iyyu domin Bugawa da Tinubu

INEC Ta Samu Karin Kungiyoyi 12 da ke Neman Rajistar Jam'iyyu domin Bugawa da Tinubu

  • Hukumar INEC ta ce ta karɓi ƙarin buƙatun ƙungiyoyi 12 da ke neman rijista a matsayin jam’iyyun siyasa
  • A dalilin hakan, a yanzu adadin ƙungiyoyin da ke jiran rijista ya haura zuwa 122, bisa bayanan hukumar
  • INEC ta bukaci ƙungiyoyin su daidaita shugabancinsu da adireshinsu don kaucewa jinkirin yi musu rajista

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar INEC ta bayyana cewa ta karɓi ƙarin buƙatun ƙungiyoyi 12 da ke neman rijista a matsayin jam’iyyun siyasa, inda hakan ya kawo adadin buƙatun zuwa 122.

Wannan ya biyo bayan sanarwar hukumar da ta fitar a ranar 23 ga Yuni, 2025, cewa ta riga ta karɓi buƙatun ƙungiyoyi 110 da ke sha’awar zama jam’iyyun siyasa a Najeriya.

Kungiyoyi 122 na bukatar INEC ta musu rajistar jam'iyya
Kungiyoyi 122 na bukatar INEC ta musu rajistar jam'iyya. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da hukumar INEC ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyu 12 na neman rajistar hukumar INEC

Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban sashen yaɗa labarai da wayar da kai, Sam Olumekun, ya ce sun samu bukatar karin rajistar jam'iyyu a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Olumekun ya ce:

“A ranar Litinin, 23 ga Yuni, hukumar ta sanar da cewa ta karɓi buƙatun ƙungiyoyi 110 da ke neman rijista a matsayin jam’iyyu.
"Mun kuma yi alkawarin ci gaba da sanar da al’umma kan halin da ake ciki.”

Daily Trust ta wallafa cewa Sam Olumekun ya ƙara da cewa:

“A ranar Laraba, 2 ga Yuli, 2025, mun sake karɓar ƙarin buƙatun ƙungiyoyi 12, lamarin da ya kai adadin zuwa 122.”

Bayanan kungiyoyin da ke son rajista

Hukumar ta bayyana cewa ta wallafa dukkan sunayen ƙungiyoyin, adireshinsu da sunayen shugabannin riko da sakatarori na wucin gadi a shafin yanar gizon INEC.

Baya ga haka, INEC ta ce an wallafa bayanan a sauran kafafen watsa labarai domin samun saukin dubawa.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

INEC ta ce za ta gudanar da nazari kan waɗannan buƙatun bisa tanadin dokar zaɓe da kuma ƙa’idojin hukumar na shekarar 2022.

Cikas da INEC ke samu a rajistar jam'iyyu

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta lura da sauye-sauyen shugabanci a wasu daga cikin ƙungiyoyin da ke neman rijista.

INEC ta ce ana samun wasu kungiyoyi na sauya sakataren riko bayan ficewarsa zuwa wata ƙungiya ta daban.

Olumekun ya ce irin waɗannan canje-canje na iya janyo tsaiko, don haka ya bukaci ƙungiyoyin da ke neman rijista su tabbatar da daidaiton shugabanci da adireshinsu.

A cewarsa:

“Domin sauƙaƙe aikin tantance waɗannan buƙatu, muna roƙon ƙungiyoyin da su daidaita sunayen shugabanninsu da adireshinsu, domin kada su jawo jinkirin duba buƙatunsu da kansu.”

INEC za ta kawo sauye sauyen zabe

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce za ta kawo wasu ka'idoji da suka shafi sakamakon zabe.

Hukumar INEC ta ce sababbin ka'idojin za su taimaka wajen tantance sakamakon zabe da aka riga aka sanar.

Hakan na zuwa ne bayan INEC ta sanar da ranaku da lokutan yin zaben cike gurbi a wasu jihohin Najeriya daban daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng