Sojoji Sun Fafata da 'Yan Ta'adda a Neja da Kaduna, An Yi Asarar Rayuka
- Rundunar sojin Najeriya ta dakile hari da ‘yan ta’adda suka kai wa sansanonin soja a jihohin Neja da Kaduna, inda aka hallaka da dama daga cikin maharan
- Amma rundunar sojojin kasar nan ta bayyana cewa a yayin fafatawar, wasu daga cikin dakarunta sun koma ga Mahaliccinsu a kokarin kare kasarsu
- Rundunar ta tabbatar da cewa an tura ƙarin dakarun soji domin ƙarfafa tsaro, tare da ci gaba da bin sawun sauran ‘yan ta’addan da suka tsere
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna –Dakarun rundunar sojin Najeriya sun dakile wani gagarumin hari da ‘yan bindiga suka kai wa sansanonin sojoji da ke jihohin Neja da Kaduna.
Sai dai harin ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji akalla 17, yayin da kuma aka hallaka da dama daga cikin maharan a musayar wuta da aka yi.

Source: Facebook
A cewar sanarwar da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na X harin ya faru ne a ranar Litinin, 24 ga Yuni, inda aka kai farmaki a wasu sansanonin sojoji guda biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kara da cewa an kai hare-haren sansanonin da ke Kwanar Dutse Mairiga da Boka a Jihar Neja, da kuma Ungwan Turai da ke Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
An gwabza tsakanin sojoji da ‘yan ta’adda
Zagazola Makama, mai bincike kan harkokin tsaro, ya bayyana a shafinsa na X cewa maharan sun kai hari daga sassa uku daban-daban a lokaci guda, lamarin da ya nuna cewa an tsara kai harin.
Sai dai sojoji sun mayar da martani cikin gaggawa ta ƙasa da sararin sama, inda suka yi amfani da ƙarfin bindiga don dakile harin.

Source: Twitter
A cewar rundunar sojin:
"Sojojin Najeriya tare da goyon bayan jiragen yaki sun yi nasarar dakile harin, suka hallaka ‘yan ta’adda da dama. Abin takaici, wasu daga cikin dakarunmu masu jarumta sun rasa rayukansu yayin kare ƙasar nan."
An jikkata sojoji a harin ‘yan ta’adda
Rundunar soji ta bayyana cewa sojoji huɗu sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga yayin artabu da maharan, kuma suna samun kulawar likitoci.
An ƙara tura ƙarin sojoji zuwa yankunan da harin ya shafa domin ƙarfafa tsaro da kuma hana maharan sake samun damar kai hari.
Rundunar ta ƙara da cewa, har yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a yankunan da harin ya auku domin cafke sauran maharan da suka tsere tare da dawo da cikakken zaman lafiya.
Sojoji sun tarwatsa wajen kera bam
A baya, mun wallafa cewa rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai wani farmaki jihar Borno, inda ta lalata sansanin da ’yan ta’adda ke hada bama-bamai da adana motocin yaki.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na sojojin, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Alhamis a birnin Abuja, ya ce an yi nasara.
A cewar Ejodame, na’urorin leken asiri sun gano wani sansani da ke yankin Kwaltiri, cikin Tumbuktu Triangle na jihar Borno, inda ake hada bama-bamai da kuma tara motocin yaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

