Kotu Ta Yanke Hukunci kan Barayin Yara a Kano, Wasu Sun Samu Shekaru 53 a Kurkuku

Kotu Ta Yanke Hukunci kan Barayin Yara a Kano, Wasu Sun Samu Shekaru 53 a Kurkuku

  • Kotu ta yanke hukunci kan mutane shida da aka kama da laifin satar yara a Kano, inda aka ɗaure su shekaru daban-daban a gidan yari
  • Kungiyar iyayen yaran da aka sace ta bayyana jin daɗinta, suna cewa hukuncin zai rage yawaitar satar yara a Najeriya, musamman Kano
  • Tsohon shugaban gungun masu satar yaran, Paul Onwe, an yanke masa hukuncin shekaru 104, yayin da aka yanke wa sauran hukunce-hukuncensu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kungiyar iyayen yaran da aka sace a Kano sun bayyana jin dadinsu da hukuncin da Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke kan mutane shida.

Kotun, karkashin Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, ta ɗaure mutanen da aka kama a gidan yari bisa laifin haɗa baki da ɓoye laifi.

An kama barayin yaran shekaru da suka gabata
Kotu ta kawo karshen shari'ar barayin yara a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Freedom Radio ta wallafa a shafinta na Facebook cewa an kama mutanen ne da satar yaran ‘yan ƙasa da shekara 10 daga hannun iyayensu, tare da sayar da su a garin Onitsha, jihar Anambra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: An yanke hukunci kan barayin yara

A zantawarsa da Legit, Kwamred Ismail Ibrahim ya shaida cewa hukuncin ya yi masu dadi, kuma zai taimaka wajen rage satar yara.

A kalamansa:

“Wannan hukunci da aka yanke wa Paul Onwe, wanda aka kama shi a shekara ta 2019 da yara guda 10, an yanke masa hukuncin shekaru 104 a gidan yari."
“Jiya aka yanke hukunci ga sauran mukarrabansa mutum shida, wanda aka yanke musu hukuncin shekaru daban-daban, wasu shekaru tara."
Barayin sun sace yara da dama a Kano
A hukuncin da kotu ta yanke, an daure wasu shekaru 55 Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ya yabawa Mai Shari’a Zuwaira Yusuf bisa tabbatarwa da adalci wajen yanke hukuncin da ya dace.

Hukuncin da kotun Kano ta yanke

An gano cewa waɗanda aka yanke wa hukunci sun haɗa da: Mercy Paul, Ebere Ogbono, Emmanuel Igwe, Loise Duru, Monica Oracha da Chinelo Ifedigwe.

An yankewa Emmanuel Igwe hukuncin shekaru 9 babu zabin tara, Ebere Ogbono shekaru 41, Monica Oracha shekaru 5 da Mercy matar Paul ta samy shekaru 55.

Sauran wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Chinelo Ifedigwe shekaru 9, sai kuma Loise Duru shekaru 6.

Tun a shekarar 2019 aka kama mutanen da ake zargi da dauke yara a Kano, sannan daga baya aka gurfanar dasu a shekarar 2020 bisa zargin laifin da suke musantawa.

Amma bayan hukuncin, an same su da satar Aisha Muhammad, Haruna Sagir, Umar Ibrahim, Amira Auwal, Husna Salisu da Usman Muhammad.

An gano wasu yaran da aka sace

A baya, mun wallafa cewa rahotanni daga jihar Borno sun tabbatar da cewa yara tara daga cikin 102 da aka sace daga sansanin gudun hijira a ranar 4 ga watan Maris 2025 sun samu nasarar kubuta.

Yaran, waɗanda ke zaune a sansanin gudun hijira, sun fada hannun Boko Haram ne yayin da suke diban itace a cikin daji domin amfanin yau da kullum da kuma tallafa wa iyayensu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta bisa sace kusan mutane 200 daga sansanin gudun hijira a Borno, tana mai yin Allah-wadai da hare-haren da Boko Haram a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.