Badaƙalar N2.5bn: EFCC Ta Cafke Tsohon Shugaban Majalisa da Wasu Ƴan Siyasa 14
- EFCC ta kama tsohon shugaban majalisar Plateau, Moses Thomas Sule, da wasu tsofaffin 'yan majalisa 14 kan badakalar N2.5bn
- An kama su ne a ranar 17 ga Yuni, 2025, biyo bayan korafe-korafe kan karya dokar halatta kuɗin haram da saba dokar sayayya
- Ana zargin tsofaffin 'yan majalisar sun karɓi motocin alfarma daga gwamnati amma suka ƙi mayar da su bayan karewar wa'adinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Plateau - Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da yi wa dukiyar jama'a zagon kasa (EFCC) ta cafke tsohon shugaban majalisar Plateau.
EFCC ta cafke Rt. Hon. Moses Thomas Sule, tare da wasu tsofaffin 'yan majalisar dokokin Plateau 14 a ranar 17 ga watan Yunin 2027.

Asali: Facebook
EFCC ta kama tsohon shugaban majalisar Plateau
A cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar a shafinta na X a ranar Laraba, 18 ga Yuni, hukumar ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A ranar Talata, 17 ga watan Yuni, 2025, jami'an hukumar EFCC reshen Makurdi sun kama tsohon kakakin majalisar Plateau, Mista Moses Thomas Sule, tare da wasu tsofaffin 'yan majalisar 14."
Sanarwar ta ce an kama tsofaffin 'yan majalisar ne bisa zargin su da aikata laifuffukan da suka shafi halatta kuɗaɗen haram da cin zarafin ofishinsu.
EFCC ta yi kamen ne biyo bayan korafe-korafe da ta samu daga wasu 'yan kishin kasa, da suka zargi tsofaffin 'yan majalisar da karya dokar halatta kudin rama ta 2022 da karya dokar sayayya.
Sunayen tsofaffin 'yan majalisa da aka kama
Tsofaffin 'yan majalisar 14 da EFCC ta cafke sun hada da: Gwottson Fom, Sani Abubakar, Jwe Philip Gwom, Thomas Dantong, da Happiness Mathew Akawu.
Sauran su ne: Cornelius Dotyok, Agbalak Ibrahim, Danjuma Azi, Fwangje Bala Ndat, Salome Tanimu Wanglet, da kuma Namba Rimuyat.
Har ila yau, tare da tsohon shugaban majalisar da aka kama, akwai tsofaffin 'yan majalisa irin su Nimchak Rims, Ishaku Maren da Paul Datugun.
Bincike da hukumar EFCC ta gudanar ya nuna cewa, tsofaffin 'yan majalisar, da suka yi aiki na watanni shida, sun samu motocin alfarma daga gwamnatin jihar da kudinsu ya kai N2.5bn.

Asali: Twitter
Dalilin kama tsofaffin 'yan majalisar Plateau
Rahoton ya nuna cewa, gwamnatin jihar Filato ta saya wa 'yan majalisar wadannan motoci ne a lokacin domin su gudanar da ayyukansu na majalisa da mazaba.
Sai dai kuma, bayan karewar wa'adinsu, 'yan majalisar sun yi mirsisi, suka ki mayar da motocin ga gwamnati, duk da kokarin da aka yi na ganin sun yi hakan.
Rahoton ya ce saboda tsofaffin 'yan majalisar sun ki mayar da motocin, dole gwamnatin jihar ta sake saya wa sababbin 'yan majalisa wasu motocin na N2bn.
EFCC ta ce wadanda ake zargin yanzu haka na hannunta kuma ana yi masu tambayoyi, yayin da ta ce za ta gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
Karanta sanarwar EFCC a nan kasa:
Kakakin majalisar Plateau ya yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban majalisar Plateau, Moses Thomas, da mataimakinsa, Gwottaon Fom, sun yi murabus.
Ana hasashen murabus ɗin nasu na da alaƙa da hukuncin da suka yanke na tsige Gwamna Caleb Mutfwang bayan rikicin siyasa a jihar.
Sake fasalin shugabancin majalisar na nuni da sauye-sauye a siyasar Filato inda majalisar ta sanar da sababbin shugabannin da ta zaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng