Tinubu: Gwanayen Musabaka Sun Samu Tagomashi, Sanata Lado Ya Masu Kyautar Gidaje

Tinubu: Gwanayen Musabaka Sun Samu Tagomashi, Sanata Lado Ya Masu Kyautar Gidaje

  • Sanata Bashir Lado ya bai wa waɗanda suka ci gasar karatun Alkur’ani sababbin gidaje domin tunawa da mahaifiyar Bola Tinubu
  • Waɗanda suka zo na farko sun samu gida mai dakuna uku da falo, yayin da na biyu suka karɓi gidaje masu dakuna biyu da falo
  • Gasar ta jawo mahalarta daga ƙananan hukumomi 44 na Kano, inda matasa sama da 100 suka shiga domin baje basirar da Allah Ya ba su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Bashir Lado, da ya shirya gasar karatun Alkur’ani don tunawa da mahaifiyar shugaban ƙasa Bola Tinubu, Hajiya Abibatu Mogaji Tinubu, ya gwamgwaje wadanda suka yi nasara.

Sanata Lado ya mika makullan gidaje sababbi fil ga mutane uku da suka nuna kwazo a gasar da ta gudana a jihar Kano a baya-bayan nan.

An gudanar da gasar Al Kur'ani a Kano
Sanata Lado ya jagoranci hada musaba a Kano Hoto: Senator Basheer Lado
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an shirya taron ne ne don girmama marigayiya Hajiya Abibatu da kuma ƙarfafa wa matasa, maza da mata giwiwa wajen haddace da kuma karanta Alkur’ani mai tsarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Lado ya gwangwaje gwarazan musabaka kyauta

Premium Times, ta wallafa cewa a yayin da yake mika makullin gidajen ga waɗanda suka ci gasar, Farfesa Ali Muhammad ya ce cewa gasar na da nufin tunawa da rayuwar Hajiya Abibatu.

Farfesa Ali Muhammad, wanda shi ne Mataimakin shugaban kwamitin shirya gasar ya bayyana gasar ta kuma cusa ƙaunar Alkur’ani a zukatan matasa.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Matasa daga dukkanin kananan hukumomin Kano sun shiga musabakar Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ya ce kyaututtukan sun haɗa da gidajen dakuna biyu da falo ga waɗanda suka zo na biyu, sannan waɗanda suka ɗauki na farko sun samu gida mai dakuna uku da falo.

An bayyana gidajen a matsayin na alfarma, kuma an gina su don ƙarfafa matasa su ci gaba da haddace Alkur’ani.

Yadda aka gudanar da musabakar Tinubu a Kano

Gasar karatun Alkur’ani ta samu mahalarta daga dukkakannin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano, inda fiye da matasa 100 suka shige ta.

Farfesa Ali Muhammad ya ce:

“Wannan kyauta wata hanya ce ta ƙarfafa wa matasa Musulmai su ci gaba da haddace da karanta Alkur’ani, su kuma ɗauki hakan a matsayin hanyar rayuwa, domin su zama nagartattun ’yan ƙasa masu kishin ƙasa.”

Waɗanda suka ci gasar su ne kamar haka: Maryam Abubakar Mu’az da ta zo ta daya a mata, Ahmad Shu’aib wanda ya zo na farko a maza.

Sai kuma Zainab Hassan Shu’aib da ta zo ta biyu a mata da kuma Ahmad Kabir Baturi da ya yi nasarar zama na biyu a maza.

An rada wa asibitin Kaduna sunan Tinubu

A wani labarin, mun wallafa cewa Gwamna Uba Sani ya sanar da radawa sabon asibitin da aka gina a Kaduna sunan Bola Ahmed Tinubu Specialist Hospital yayin da Shugaban ya kaddamar da aikin.

A cewar wata sanarwa da fadar shugaban ƙasaya fitar, ta kar ada bayyana cewa an sanya wa asibitin suna ne domin karrama shugaba Tinubu bisa irin nagartaccen jagoranci.

Sabon asibitin, wanda aka gina a cikin birnin Kaduna, na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kiwon lafiya da ke da nufin inganta samar da lafiya ga jama’ar jihar da ma Najeriya baki ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.