Najeriya Ta Aikata Manyan Laifuffuka, ECOWAS Ta Ci Kasar Tarar Naira Miliyan 20
- Kotun kungoyar ECOWAS ta ce Najeriya ta keta haƙƙin ɗan kasuwa Moses Abiodun wanda aka tsare tun 2009 ba tare da shari’a ba
- An bayyana cewa SARS ta kama shi a Legas cikin 2008, aka tsare shi kurkukun Legas ba tare da an gurfanar da shi ba tsawon shekaru 16
- Kotun ta umurci a saki Abiodun tare da biyan sa Naira miliyan 20 a matsayin diyya, bayan tan kira tsarewar da 'azabtarwa da 'cin mutunci'
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kotun shari’a ta ECOWAS ta yanke hukunci a kan Mista Moses Abiodun, wani ɗan kasuwar Najeriya da aka tsare tun 2009 ba tare da shari’a ba.
Kotun ta bayyana cewa Tarayyar Najeriya ta keta haƙƙoƙin ɗan Adam na Mista Moses Abiodun a wurare da dama.

Asali: Twitter
'Dan kasuwa ya yi karar Najeriya a kotun ECOWAS
Moses Abiodun ya kai ƙara gaban kotun ECOWAS yana zargin cewa 'yan sanda na sashen SARS ne suka kama shi a watan Nuwamba 2008, inji rahoton Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce tun daga lokacin ake tsare da shi, inda aka fara riƙe shi na watanni biyar ba tare da tuhuma ba, kafin wata kotun majistare a jihar Legas ta tsare shi a ranar 23 ga Maris, 2009.
Abiodun ya koka cewa duk da shafe shekaru 16 yana tsare, ba a taɓa gurfanar da shi a gaban kuliya ko zartar da hukunci a kansa ba.
Ya kuma bayyana cewa tsare shi har na tsawon shekaru 16 ya keta haƙƙin ɗan adam da dokar tsarin Afirka da kuma ƙa’idojin ƙasashen duniya da Najeriya ta sanya hannu a kai.
Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin, tana shakkar sahihancin takardar umarnin tsarewar da mai ƙara ya gabatar, tare da ƙalubalantar karɓar karar.
Kotun ECOWAS ta kama Najeriya da laifuffuka
Sai dai tun da fari, kotun ECOWAS ta ce tana da hurumin sauraron wannan shari’ar, kuma ta karbi takardun da mai kara ya gabatar saboda cika ka’ida.
Bayan nazari, kotun ta tabbatar cewa ci gaba da tsare Moses na tsawon shekara 16 ba tare da tuhuma ko shari’a ba ya saba da sashe na 6 na dokar Afrika da sashe na 9 na yarjejeniyar ICCPR.
Kotun ta kuma gano cewa wannan tsarewar da aka yi masa ya keta ‘yancinsa na zirga-zirga kamar yadda aka tanada a sashe na 12 na dokokin da suka shafi ‘yancin ɗan adam.
Dangane da rashin samun shari’a mai adalci, kotun ta ce tsare mutum har na shekara 16 ba tare da shari’a ko tuhuma ba babban tauye haƙƙin ɗan adam ne da ya saba da sashe na 7(1)(d) na dokar Afirka.

Asali: Twitter
Kotu ta ci tarar Najeriya Naira miliyan 20
Kotun ta ƙara da cewa irin wannan tsarewa ba tare da hukunci ba tamkar hukunci ne kafin shari’a, kuma haka ya zama azabtarwa da cin mutuncin ɗan Adam, wanda ya saba da sashe na 5 na yarjejeniyar Afirka da sashe na 7 na ICCPR.
A ƙarshe, kotun ta ECOWAS ta yanke hukuncin cewa an keta haƙƙin ɗan adam na Moses Abiodun, ta kuma ba da umarnin a sake shi nan take, tare da biyan sa Naira miliyan 20 a matsayin diyya.
Hukuncin ya fito ne daga alkalan kotun uku: Hon. Justice Sengu Koroma (shugaban zaman), Hon. Justice Gbéri-bè Ouattara, da Hon. Justice Edward Asante.
Kotun ECOWAS ta yi hukunci kan dokar batanci
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotun ECOWAS ta yanke hukunci cewa dokokin batanci na jihar Kano sun ci karo da dokokin kare haƙƙin ɗan Adam na duniya.
Ta ce dokokin da ke cikin kundin laifuffuka da na Shari’ar Musulunci na jihar sun takurawa ’yancin faɗin albarkacin baki da walwalar jama’a.
Kotun ta umarci gwamnatin tarayya da ta soke ko ta gyara dokokin, waɗan da ra ce suna haddasa kama mutane, tsare su ko kuma yanke masu hukuncin kisa ba bisa doka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng