Ana Jimamin Tashin Bam, Almajirai Sun Rasu bayan Sun Sha Wani Abu a Kano
- Ɗalibai biyu na makarantar koyon Alqur'ani waɗanda aka fi sani da almajirai sun rasa rayukansu bayan shan wani abu da ake zargin akwai guba a Kano
- Rahoto ya nuna cewa almajiran sun zuba wani sinadari a cikin shayi ranar Laraba, daga nan suka fara rashin lafiya mai tsanani
- Wani ɗan unguwar da abin ya faru ya ce yaran sun riƙa fitar da kumfa daga bakinsu, wanda ya sa ake zargin guba suka sha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Wani mummunan lamari ya afku a unguwar Gwammaja, titin Kotu, cikin birnin Kano, inda wasu ɗaliban makarantar tsangaya watau Almajirai guda biyu suka rasa rayukansu.
Almajiran guda biyu, Abdullahi mai shekaru 12 da Aminu mai shekaru 14 sun rasu ne bayan sun sha wani abu mai guba.

Asali: Original
Tribune Online ta tattaro cewa bayan waɗanda suka rasu, wasu almajirai hudu na kwance a asibiti suna jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me almahiran suka sha a shayi a Kano?
Lamarin wanda ya afku ranar Juma'a bayan almajiran sun sha wani abin da suka dauka madarar gari ce, da wani ya jefo cikin gidansu ta katanga.
Malaminsu na Qur’ani, Malam Nafiu, ya bayyana cewa:
“Yaran sun zuba wannan sinadari a cikin shayi a ranar Laraba, jim kaɗan bayan sun gama sha sai suka kamu da rashin lafiya mai tsanani.
"Wani ya jefo sinadarin daga bayan katanga, yana daga cikin abubuwan da ake amfani da su a cikin shayi. Yaran sun dauka madara ce. Hudu daga cikinsu sun farfado, amma Abdullahi da Aminu sun rasu.”
Malam Nafiu ya kara da cewa, yaran biyu da suka mutu sun fito ne daga karamar hukumar Dandume a jihar Katsina, kuma an kawo su Kano domin koyon karatun Qur’ani.
Wane mataki aka ɗauka kan mutuwar almajirai?
Wani ganau wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa, “An ga kumfa na fita daga bakunan yaran da suka mutu, wanda hakan ya kara janyo zargin cewa guba ce suka sha.”
“Ainihin dalilin mutuwar bai tabbata ba tukuna, har sai an kammala gwajin binciken guba da kuma gwajin gawa," in ji shi.

Asali: Getty Images
Wani mazaunin unguwar, Tahir Majid, ya bayyana alhini da bakin ciki kan lamarin, yana mai cewa:
“Wannan abu ya girgiza mu. Yaran nan masu ladabi ne kuma masu kokari, irin haka ba ta taɓa faruwa a unguwarmu ba, Muna kira ga hukumomi da su binciko gaskiya game da mutuwar yaran.”
Ya kara da cewa tuni aka sanar da iyayen yaran da suka mutu, kuma ana sa ran za su iso daga Dandume, jihar Katsina, kamar yadda PM News ta rahoto.
A lokacin da ake hada wannan rahoto, gawarwakin yaran na nan a gidan malaminsu suna jiran gudanar da sallar jana’iza bayan an kammala binciken farko.
Bam ya halaka mutum 5 a Kano
A wani labarin, kun ji cewa aƙalla mutane biyar ne suka rasa ransu da wani bam ya tawatse a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
Lamarin ya afku a safiyar Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025 a hanyar Eastern by pass, a daidai wani kamfanin yan gwangwan da ke yankin.
Kwamishinan yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori da ya tabbatar da al'amarin ya ce an kwashi mutane 15 zuwa asibiti.
Asali: Legit.ng