Kano: Kotu Ta Tasa Ƙeyar Ɗan TikTok da Ke Shigar Ƴan Daudu zuwa Gidan Kaso
- Karyar wani dan TikTok ta kare bayan wata kotu a Kano ta yanke masa hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso
- Ana zargin dan TikTok din mai suna Abubakar Kilina kan ɗaukar bidiyon rashin ɗa’a da kuma shigan yan daudu
- Kilina ya gurfana gaban kotu bayan hukumar tace fina-finai ta Kano ta kai kara bisa amfani da kalmomi da halayen batsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wata kotun majistare da ke zaman ta a Kano ta daure dan TikTok a gidan kaso kan yaɗa badala.
Kotun karkashin jagorancin Majistare Hadiza Muhammad Hassan ta yanke hukuncin ne a jiya Alhamis 19 ga watan Yunin 2025.

Asali: UGC
Tribune ta ce kotun Lamba 21, ta yanke wa Abubakar Usman Kilina hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ake kokarin kawar da badala a Kano
Ana yawan daure 'yar TikTok a Kano saboda zargin yaɗa badala da suke a mafi yawan bidiyo da suke yi.
Hakan ya biyo bayan kokarin da gwamnati ke yi na tabbatar da an kawar da badala a fadin jihar da taimakon hukumar Hisbah.
Hukumar tace fina-finai ta Kannywood karkashin jagorancin Abba Al-Mustapha ta sha daukar matakai kan daraktoci da jarumai domin tabbatar da bin doka da oda.

Asali: Original
Musabbabin daure Kilina a gidan yarin Kano
An samu Kilina da laifin tallata dabi'u marasa kyau da kuma saka masu sanya kaya irin na mata a matsayin dan daudu.
A daya daga cikin bidiyon TikTok dinsa an gano yadda yake amfani da kalmomin batsa wanda haka ya saba ka'ida da kuma al'adar Hausawa da jihar Kano.
Hukuncin ya biyo bayan karar da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano karkashin kulawar Abba Al-Mustapha ta shigar a kansa kan laifin karya dokar da'a da cin mutunci, cewar Daily Post.
Wane zabi kotun ta ba dan TikTok din?
Sai dai kotun ta ba shi zaɓin biyan tarar N100,000 tare da diyyar N30,000 ga hukumar tace fina-finai saboda bata musu lokaci kan korafin da suka shigar.
Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, Hadiza ta ja kunnen Kilina da ya guji duk wani abu da ke sabawa tarbiyya da halayyar al’umma da doka musamman a jihar.
Ta kara da cewa idan har ya kara aikata irin wannan laifi, kotu ba za ta sake ba shi zabin biyan tara ba kuma za ta aiwatar da cikakken hukunci ba tare da rangwame ba.
An kama yan TikTok kan wallafa batsa
Mun ba ku labarin cewa wasu fitattun ƴan TikTok uku a jihar Kano sun shiga matsala sakamakon wallafa hotuna da bidiyon rashin ɗa'a.
Wata kotu a Kano ta kama ƴan TikTok ɗin da laifin haɗa baki wajen aikata laifi da yaɗa hotuna batsa marasa kyawun gani.
Mai Shari'a Halima Wali ta yanke masu hukunci ɗauri a gidan yari na tsawon shekara ɗaya da wata guda ko su biya tara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng