'Ƴar TikTok Ta Yi Wani Irin Mutuwa Mai Ban Tausayi, an Samu Gawarta a Dakinta
- Kamfanin Teleperformance a Kenya ya musanta zargin hana wata ƴar TikTok, Ladi Olubunmi, izinin zuwa hutunta a gida Najeriya
- An tsinci gawar Olubunmi a cikin gidanta bayan kwana uku da rasuwarta, inda ta riga mu gidan gaskiya a wani yanayi mai ban tausayi
- Abokanta sun bayyana cewa ta dade tana nuna gajiya da rashin lafiya, tana kuma kokarin komawa Najeriya domin hutu kafin ta rasu
- Fiye da 'yan Najeriya 100 da ke aiki a karkashin Teleperformance ba su da takardar izinin aiki da ke hana su zuwa gida har tsawon shekaru
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Nairobi, Kenya - Wani kamfani da ke wakiltar manhajar TikTok a Kenya, Teleperformance ya musanta zargin hana wata ‘yar Najeriya, Ladi Olubunmi, izinin tafiya hutu.
Rahotanni sun bayyana cewa an gano gawar Olubunmi a cikin gidanta a makon da ya gabata, bayan kwana uku da rasuwarta.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Kaduna, an samu asarar rayuka

Asali: Facebook
Kamfani ya kare kansa bayan mutuwar ƴar TikTok
ABC news ta ce Teleperformance na Kenya, wani kamfanin Faransa da TikTok ke aiki da shi inda ya musanta zargin hana ta komawa Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma kafafen watsa labarai na duniya sun nuna akasin haka, abokan aikinta suka ce ta sha nuna gajiya kuma tana son komawa gida.
Duk da tana da damar samun tikitin komawa gida duk shekara, an ce an hana ta tafiya saboda matsalar takardar izinin aikinta.
Kauna Malgwi, daya daga cikin abokanta, ta kara bayyana cewa fiye da 'yan Najeriya 100 ba su da takardar izinin aiki tsawon shekaru biyu.
Ta ce:
“Fiye da ‘yan Najeriya 100 ne ke aiki da Teleperformance ba tare da takardar izinin aiki ba tsawon shekaru biyu."

Asali: UGC
An karrama marigayiyar bayan mutuwarta
Bayan rasuwarta mai cike da alhini, ma’aikatan fasaha a Kenya sun gudanar da taron tunawa da ita tare da bayyana damuwa kan yanayin aiki.
Kokarin samun martani daga Hukumar NiDCOM bai yi nasara ba, domin kakakinta bai amsa kira ko tambaya ba.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ba wannan ne karon farko da yan Najeriya ke mutuwa a yanayi mai ban mamaki a kasar Kenya ba.
A watan Yuli na 2021, wasu ‘yan Najeriya biyu sun mutu a wata liyafa a gida a yanayi da ba a fayyace ba.
Daya daga cikinsu ya faɗo daga bene na bakwai na gidan Skyhorse a Kilimani, ya mutu nan take, yayin da dayan ya fadi a madafi.
Kotu ta daure ƴar TikTok kan batanci
Kun ji cewa wata kotu a Indonesia ta yanke wa Ratu Thalisa hukuncin daurin shekaru biyu da watanni 10 a gidan yari bisa batanci ga Annabi Isa dan Maryam.
An ce ana tuhumr Thalisa ne bayan ta yi hira da hoton Annabi Isa a TikTok tana cewa ya aske gashinsa wanda ya jawo hayaniya a kasar.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama, ciki har da Amnesty International, sun soki hukuncin tare da kira a soke shi saboda kowa yana da ƴancin albarkacin bakinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng