Sauƙi Ya Samu: Gidajen Mai 6 a Najeriya Sun Sauke Farashin Fetur zuwa Ƙasa da N870

Sauƙi Ya Samu: Gidajen Mai 6 a Najeriya Sun Sauke Farashin Fetur zuwa Ƙasa da N870

  • Farashin fetur a manyan gidajen mai shida da ke haɗin gwiwa da matatar Dangote ya faɗi ƙasa idan aka kwatanta da farashin NNPCL
  • Dangote ya haɗa gwiwa da dillalan fetur da dama don tabbatar da samar da kayayyakin man fetur a farashi mai araha ga 'yan Najeriya
  • Haka kuma, matatar ta sanar da shirin fara raba fetur da dizal kyauta ga abokan huldarta, matakin da ya jawo suka daga wasu dillalai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Manyan dilolin mai, Ardova Plc da MRS Oil Nigeria Plc, waɗanda dukkansu abokan huldar matatar Dangote ne, sun rage farashin fetur zuwa N865 a gidaje man su.

Gidajen man sun rage farashin zuwa N865 daga N870 da ake sayar da shi, wanda hakan ya sake sanya su zama matsayin wuraren samun man fetur mafi arha.

MRS da gidajen mai 5 sun sauke farashin litar fetur zuwa N865
Gidan man MRS da wasu 5 sun sauke farashin fetur kasa da na NNPCL. Hoto: Bloomberg/Getty Images
Asali: Getty Images

Gidajen mai 6 sun rage farashin fetur

Wani ma'aikacin gidan man MRS, Ajumoke, ya shaida wa wakilin jaridar Legit.ng cewa an fara amfani da sabon farashin ne a ranar Litinin, 16 ga Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajumoke ya bayyana cewa:

"Shugabanmu ya yi gyare-gyaren ne a safiyar Litinin, bisa umarni daga babban ofishinmu."

An ce sauran abokan huldar Dangote kamar Technooil, Optima Energy, Hyde, da Heyden suma sun yi wadannan sauye sauye.

Sai dai har yanzu gidajen sayar da man NNPCL suna sayar da litar fetur a kan N870, yayin da gidajen man Mobil suka ɗan rage farashinsu daga N875 zuwa N870.

Matatar Dangote ta rage farashin fetur

Tun da fari, matatar Dangote ta rage farashin da take sayarwa abokan huldarta mai zuwa N838 a kan kowace lita a ranar Litinin, daga N840 da ta sayar a makon da ya gabata.

Dangote yana sayar da fetur a wannan farashin ne kawai ga abokan huldarsa, wadanda ke dakonsa daga matatarsa ko rumbunan ajiyar mansa.

Ana ganin sauke farashin da Dangote ya yi zuwa N838 ne ya sanya abokan huldarsa, irin su MRS da Ardova suka yi gaggawar sauke farashin a gidajen man su.

Gidajen man MRS da wasu 5 sun sauke farashin fetur ne bayan Dangote ya sauke na shi farashin
MRS da wasu diloli 5 ne manyan abokan huldar matatar man Dangote. Hoto: Bloomberg/Getty Images
Asali: UGC

PENGASSAN ta ce ana zaluntar 'yan Najeriya

Duk da ragin da aka samu, kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta ce ana zaluntar 'yan Najeriya a harkar sayar masu da fetur.

Mun ruwaito cewa, PENGASSAN ta ce bai kamata kamata a rika sayarwa 'yan Najeriya litar fetur a kan N900 ba, kyau a ce a sayar da shi tsakanin N700 zuwa N750.

Shugaban ƙungiyar, Festus Osifo, ya koka kan cewa farashin danyen mai a duniya ya faɗi zuwa kusan $60 a kan kowace ganga, amma gidajen mai a Najeriya sun ki sauke farashin fetur.

Farashin litar fetur zai iya sauka kasa da N700

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu manyan ƴan kasuwa sun cimma yarjejeniya da masu samar da fetur daga ƙasashen waje, domin shigo da fetur mai rahusa zuwa Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa sabon tsarin shigo da fetur ɗin na iya rage farashin litar man fetur zuwa kimanin N700 a Najeriya.

Shugaban kungiyar PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya bayyana cewa hauhawar farashi a matatar Dangote na tilasta wa ƴan kasuwa neman mafita daga ƙasashen waje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.