Bayan Fara Biyan Sabon Albashi, Gwamna Zai Kashe N63.4bn a Gyara Gidan Gwamnati

Bayan Fara Biyan Sabon Albashi, Gwamna Zai Kashe N63.4bn a Gyara Gidan Gwamnati

  • Gwamnatin Oyo ta amince da kashe N63.479bn don gyaran gidan gwamnati, wanda ta bayyana cewa yana cikin mawuyacin hali
  • Gwamnati za ta kuma gyara babban zauren taron gidan gwamnatin kafin bikin cika shekaru 50 da kafuwar jihar a shekarar 2026
  • Majalisar zartarwar jihar ta amince da biyan kuɗin gina babbar kasuwar kayan gona da kuma N130m don ayyukan hukumar ci gaban birane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Majalisar zartaswar jihar Oyo a ranar Laraba, ta amince da kashe N63.479bn don gyara gine-ginen da ke cikin gidan gwamnatin jihar.

Kwamishinan Labarai na Oyo, Dotun Oyelade, ya bayyana a Ibadan, yana mai cewa majalisar ta ga dacewar gyara gidan gwamnatin "saboda yana cikin mawuyacin hali".

Gwamnatin Seyi Makinde za ta kashe N63.4bn don gyara gidan gwamnatin Oyo
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde zai gyara gidan gwamnati kan N63.4bn. Hoto: @seyiamakinde/X
Asali: Facebook

Dotun Otelade ya ce tsawon shekaru shida da suka gabata, gwamnan da mataimakinsa suke zaune a gidajensu maimakon na gwamnati, a cewar rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gyare gyare a gidan gwamnatin jihar Oyo

Oyelade ya ce za a kammala babban dakin taron gidan gwamnati kafin bikin cika jihar shekaru 50 da kafuwa a 2026, a matsayin wani ɓangare na gadon da Gwamna Seyi Makinde zai bar wa gwamna mai zuwa.

Kwamishinan ya ce:

"Majalisar ta kuma amince da kashe N131.751m don ɗaukar ƙwararrun ma'aikatan lambu da za su riƙa kula da fulawowi da shukokin da ke cikin gidan gwamnati."
"Haka kuma, don cika alƙawarinta na haɓaka filin jirgin sama na Samuel Ladoke Akintola, gwamnati ta fara aikin sanya na'urorin saukar jiragen sama (ILS)."

Dotun Oyelade ya kuma ce an lalata wata na'ura da gwamnatin tarayya ta saya a filin a baya, kuma jihar ta ɗauki nauyin saye da sanya wata sabuwar na'urar cikin watanni shida.

Kwamishinan ya sake jaddada cewa ana samar da kayan aiki ga hukumar Kwastam, hukumar shige da fice da sauran muhimman hukumomi don tallafawa ayyukansu.

Gwamna Seyi Makinde zai gina katafiyar kasuwar amfanin gona a Oyo kafin wa'adinsa ya kare
Gwamna Seyi Makide ya kara yawan kasafin jihar Oyo na 2025. Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

Sababbin ayyukan jihar da batun kasafin 2025

A wani jikon, majalisar zartaswar ta kuma amince da biyan kuɗin farko na yarjejeniyar gina kasuwar abinci da kayan noma ta duniya, wadda za a gina a Ijaiye, Ibadan.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnatin jihar Oyo da hadin gwiwar Bankin Raya Afirka ne za su gina wannan katafariyar kasuwar baje kolin kayayyakin gona.

Kwamishinan ya kuma ce an amince da fitar da N130m a matsayin wani kaso na ayyukan sabuwar hukumar ci gaban kauyuka da birane ta jihar.

Dotun Oyelade ya kuma bayyana cewa kasafin kuɗin jihar na 2025 ya ƙaru da N270.854bn don ba gwamnatin damar kammala ayyukan da ke gudana kafin ƙarshen wa'adin Seyi Makinde.

Gwamnan Oyo ya fara biyan sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, farin ciki ya mamaye ma’aikatan jihar Oyo bayan Gwamna Seyi Makinde ya fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000.

Wannan mataki ya nuna cikar alƙawarin da gwamnatin jihar ta dauka na inganta walwalar ma’aikata da fitar da su daga kuncin rayuwa daga Janairun 2025.

Ba wai ma’aikata ne kawai suka amfana da sabon mafi karancin albashin ba, hatta masu karɓar fansho sun samu karin albashi fiye da yadda aka saba biyansu kowane wata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.