Hotunan kayatattun birane 8 a Afrika da ke gogayya da Turai
Ana kallon nahiyar Afrika a matsayin nahiyar da ta fi kowacce talauci a duniya. Amma kuma, wadannan kyawawan birane a Afrika za su iya gogayya da wasu manyan biranen kasashe masu tarin arziki a duniya.
A kafafen sada zumuntar zamani, mun saba ganin hotunan 'yan Afrika a yunwace a cikin tagayyararrun kauyuka.
Da yawa daga mutanen duniya irin wadannan hotunan mutanen suke gani, kuma suke kwatanta Afrika da shi. Amma kuma ba haka abun yake ba a wasu sassan nahiyar da yawa.
Akwai birane a Afrika da za su iya bata labarin da aka sani game da ita kuma su yi fito na fito da manyan biranen duniya. Ga wasu daga ciki:
1. Luanda, Angola
Luanda ce babban birnin kasar Angola kuma cibiyar samar da man fetur ta uku a Afrika. Ita ce ke dauke da filin jirgin ruwa na kasar da kuma cibiyar mulki.
Gwamnatin kasar na kashewa garin kudi ta hanyar yin kasaitattun gine-gine tare da gyare-gyare. Tana gyara manyan hanyoyi kuma ta fara gina wani mashahurin filin sauka da tashin jiragen sama a 2019.

Asali: Getty Images
2. Johannesburg, Afrika ta Kudu
Birnin Johannesburg katafare ne kuma mafi arziki a kasar Afrika ta Kudu. Yana cike da manyan al'adu kuma babu shakka wannan 'aljanna' ce ga masu yawon bude ido.

Asali: Getty Images
3. Dar Es Salaam, Tanzania
Babban birnin kasuwanci ne da mulki. Dar Es Salaam ne babban birni kuma mafi arziki a Tanzania.

Asali: Getty Images
4. Nairobi, Kenya
Birnin Nairobi ya saba karbar masu yawon bude ido. Wuri ne da ke da damammaki na kasuwanci da shakatawa.

Asali: Getty Images
5. Marrakech, Morocco
Marrakech na daya daga cikin manyan biranen duniya wanda ke da ababen mamaki.
Ginin birnin ja ne kuma yana da fadoji, masallatai da kuma kasuwanni. Babu shakka Marrakech na daya daga cikin birane mafi kyau a Afrika.

Asali: Getty Images
6. Cape Town, Afrika ta Kudu
Birnin yana nan a kusa da wani tsauni, ba a iya kwatanta kyan shi ballantana idan rana ta fito.
7. Tunis, Tunisia
Wannan shine masaukin manyan ofisoshi da tituna masu kyau. Ziyara a kasar Tunis za ta tunatar da kai tsibirin Girka da Andalusia na Spain.

Asali: Getty Images
8. Abuja, Najeriya
Abuja gida ne na tsafta da manyan tituna. Akwai manyan gine-gine tare da babban masallacin kasar Najeriya.

Asali: UGC
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng