Bayan Shafe Fiye da Shekara a Gidansa, Gwamnan PDP Ya Shiga Gidan Gwamnati, Ya Fadi Dalilai

Bayan Shafe Fiye da Shekara a Gidansa, Gwamnan PDP Ya Shiga Gidan Gwamnati, Ya Fadi Dalilai

  • A karshe, Gwamna Ademola Adeleke ya shiga gidan gwamnatin jihar da ke birnin Osogbo bayan kammala kwaskwarima
  • Gwamna Adeleke ya shafe shekara daya da watanni hudu a gidansa da ke Ede, kusa da birnin Osogbo da ke jihar Osun
  • Wannan mataki na gwamnan ya jawo suka daga jam’iyyar adawa ta APC ganin yadda ya dauki lokaci ba a gidan gwamnatin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun – Bayan shafe shekara daya da watanni hudu da karbar rantsuwa, Gwamna Ademola Adeleke ya shiga gidan gwamnati.

Gwamnan kafin shiga gidan gwamnatin ya na rayuwa ne a gidansa da ke Ede, wani kauye kusa da birnin Osogbo a jihar Osun.

Kara karanta wannan

Malaman jami'a karkashin SSANU za su shiga yajin aiki, sun fadi yaushe za su dawo

Gwamnan PDP ya tare zuwa gidan gwamnati bayan shafe fiye da shekara a gisansa
Gwamna Ademola Adeleke na Osun ya koma gidan gwamnati da zama. Hoto: Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

Yaushe Adeleke ya kama aiki a matsayin gwamna?

Adeleke ya karbi rantsuwa a ranar 27 ga watan Nuwambar 2022, tun a wancan lokacin bai shiga gidan gwamnatin jihar ba, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da matsin lamba da kushewa daga jam’iyyar adawa ta APC a jihar, Adeleke ya ci gaba da zama a gidansa inda ya ke gudanar da gwamnati.

Punch ta tattaro cewa gwamnan ya ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati a gidansa da nufin cewa ana gyara a gidan gwamnatin.

Kakakin gwamnan, Adewale Rasheed ya ce an kammala gyaran gidan gwamnatin kuma gwamnan ya shiga daga ciki.

Dalilin kin shiga gidan gwamnatin Osun

Adewale ya bayyana haka ne a yau Lahadi 17 ga watan Maris inda ya ce an dade ana gyaran dukkan gidan gwamnatin ne gaba daya.

Ya ce an gyara gidan gwamnatin ne saboda ceto shi daga rugujewa bayan halin da gwamnatin ta same shi yayin da ta karbi mulki.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 16: Gwamnan PDP ya yi martani kan harin, ya fadi abin da zai yi kan lamarin

Gwamna ya kuma yi alkawarin cewa zai kammala dukkan ayyukan da aka fara ba a karisa ba a jihar domin al’umma, cewar Mouthpiece.

An kaddamar da abinci mai rahuwa a Legas

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Legas ta lissafo kasuwannin da al’ummar jihar za su samu kayan abinci mai rahusa.

Idan ba a manta ba, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya rage farashin kayan abinci da kaso 25 a fadin jihar baki daya.

Wannan mataki na gwamnan na zuwa ne bayan ganin halin da ‘yan jihar ke ciki na tsadar kayan masarufi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel