Manoma Sun Shiga Uku, Lakurawa Sun Ƙaƙaba Musu Takunkumi da Barazanar Kisa

Manoma Sun Shiga Uku, Lakurawa Sun Ƙaƙaba Musu Takunkumi da Barazanar Kisa

  • Mayaƙan ƙungiyar Lakurawa sun kakaba takunkumi a kauyuka da dama a Augie da ke jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa mayakan sun hana manoma sayar da shanu don siyan injin huɗa na fetur a yankin
  • Sun bayyana cewa duk wanda ya sayar da shanunsa zai iya rasa rayuwarsa, lamarin da ya sanya fargaba a zukatan mazauna yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin-Kebbi, Kebbi - Manoma da dama a wasu yankunan jihar Kebbi sun shiga damuwa kan takunkumi daga kungiyar Lakurawa.

Mayaƙa ƙungiyar sun mamaye fiye da ƙauyuka goma a yankin Augie da ke Jihar Kebbi domin tabbatar da cewa sun bi umarnin.

Lakurawa sun sanya takunkumi ga manoma
Lakurawa sun sanya manoma cikin wani hali a Kebbi. Hoto: Legit.
Asali: Original

Rahoton BBC Hausa ya ce mayakan sun hana jama’a sayar da shanunsu a wannan damina da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yan bindiga ke sanya takunkumi a Arewa

Wannan ba shi ne karon farko ba da yan bindiga ke kakabawa manoma da sauran mazauna yankuna takunkumi a Arewacin Najeriya.

Sau da dama mayakan na ƙaƙaba haraji da manoma ko sauran al'umma da ke rayuwa a yankunan da suke domin karin samun kudin shiga.

Ko a kwanakin nan ma riƙaƙƙen ɗan bindiga, Bello Turji ya kakabawa wasu mazauna ƙauyuka a jihar Zamfara harajin N50m.

Turji ya bukaci makudan miliyoyin ne daga mazauna Tsallaken Gulbi da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.

Wadanda abin ya shafa sun hada da mutanen kauyen Fakai har zuwa Qaya da ke kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

An tabbatar da cewa Turji ya bukaci kudin ne domin ya bar su su ci gaba da noma a wannan kakar ba tare da sun samu matsala ba.

Lakurawa sun addabi al'umma a Kebbi
Kungiyar Lakurawa sun sanya takunkumi ga manoma a Kebbi. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Manoma sun shiga firgici kan umarnin yan bindiga

Manoman suka ce duk wanda ya sayar da shanunsa zai iya baƙuntar lahira ba tare da bata lokaci ba, cewar Leadership Hausa.

Wasu manoma sun ce sun saba sayar da dabbobinsu don guje wa satar da ‘yan bindiga ke yi, amma yanzu sun rasa mafita.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa suna sayar da shanu don su mallaki injin noman shinkafa, amma yanzu dole su saurari umarni.

“Idan suka shigo gari a kan mashin, uku ne a kan kowanne, bindiga a hannu, kuma sukan kwashe dabbobi har da kaji, mutum kuma baya iya cewa uffan."

- Cewar wani mazaunin yankin

Yanzu haka muna cikin fargaba a yankin, kuma jama’a na roƙon gwamnati da jami’an tsaro su tashi tsaye wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Kebbi

Kun ji cewa an shiga jimami a jihar Kebbi biyo bayan wani mummunan harin ta'addancin da ƴan bindiga suka kai kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ƴan bindigan sun hallaka mutane da dama a yayin harin wanda suka kai a ƙauyen Tadurga da ke ƙaramar hukumar Zuru.

Maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane zuwa cikin daji, tare da sace shanu a harin wanda suka kai cikin dare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.