"Ba Atiku bane": Gwamna Dauda Ya Fadi Abin da Ya Haddasa Rikicin Jam'iyyar PDP
- Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ta yi magana kan rikicin da ya daɗe yana addabar jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
- Dauda Lawal ya bayyana cewa rikicin na PDP ya wuce batun a ce matsala ce ta mutum ɗaya, sai dai girman kai da ya yi wa mambobin katutu
- Gwamnan na jihar Zamfara ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa za a warware rikicin domin suna ƙoƙarin ganin an cimma hakan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin da ke addabar jam’iyyar PDP ya wuce batun ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar.
Dr. Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa rikicin na PDP ya samo asali ne daga girman kai tsakanin mambobin jam’iyyar.

Asali: Twitter
Gwamna Lawal ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba a jihar Zamfara, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Gwamna Dauda ya ce kan rikicin PDP?
Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa matsalar ba ta tsaya ga mutum guda ba.
"Duk wanda ka gani yana da ta shi matsalar, ba wai game da Atiku Abubakar kaɗai bane, lamarin ya wuce nan."
"Wannan rikici yana cikin jam’iyyar PDP ne a matsayin rikicin cikin gida, kuma muna ƙoƙarin warware shi. Ina ganin girman kai ne ke haddasa hakan, kowa yana da nasa, babu wanda aka bari."
- Gwamna Dauda Lawal
Da aka tambaye shi ko shi ma yana cikin waɗanda ke da hannu wajen haifar da wannan rikici na girman kai, Gwamna Dauda Lawal ya amsa da cewa “Eh.”
Gwamna Dauda ya taɓo batun zaɓe
Yayin da ya ke karin bayani kan tsarin zaɓe a Najeriya, Gwamna Dauda Lawal ya nuna cewa yana da kyakkyawan fata cewa zaɓe mai inganci da gaskiya zai ci gaba da yiwuwa duk da matsalolin da ake fuskanta.
Ya bayyana cewa nasarar da ya samu a matsayin ɗan takarar PDP na farko da ya lashe gwamnan jihar, wata shaida ce ta sahihancin tsarin zaɓe yayin da ake shirin fuskantar zaɓen 2027, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Asali: Facebook
“Ina ganin za a ci gaba da samun zaɓe na gaskiya da adalci. Hakan ne ya sa na lashe zaɓen gwamna a Zamfara. Ni ne gwamnan PDP na farko da aka zaɓa a jihar Zamfara."
"Saboda haka, zaɓen ya kasance sahihi kuma na gaskiya, kuma ina da yakinin hakan zai sake faruwa. A jira lokaci kawai."
- Gwamna Dauda Lawal
Damagum ya musanta shirin ficewa daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum, ya yi magana kan jita-jitar cewa yana shirin komawa APC.
Damagum fito ya ƙaryata jita-jitar wadda ta ce ya shirya tsaf domin komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Muƙaddashin shugaban na PDP ya bayyana cewa maƙiyansa na siyasa ne ke yaɗa irin waɗannan rahotannin a ƙoƙarin da suke yi na ɓata masa suna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng