Kano: Mota Ta Murkushe Mai Kwacen Waya Jim Kadan Bayan Fauce Wayar Wata, Ya Shiga Kakani-Kayi

Kano: Mota Ta Murkushe Mai Kwacen Waya Jim Kadan Bayan Fauce Wayar Wata, Ya Shiga Kakani-Kayi

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cewa mota ta buge wani mai kwacen waya a jihar bayan ya yi fashi
  • Matashin ya gamu da tsautsayin ne jim kadan bayan kwace wayar inda ya yi kokarin tsallaka titi a Zoo Road da ke birnin
  • Legit Hausa ya tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a jihar kan sanin halin da ake ciki amma bai yi martani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsautsayi ta rutsa da wani matashi bayan ya kwace wayar wata mata a jihar Kano.

Matashin ya gamu da tsautsayin inda mota ta murkushe shi jim kadan bayan kwace wayar don tsallaka titi.

Kara karanta wannan

Kaduna: Masu garkuwa sun tsare tsohon shugaban makaranta da ya tafi kai kudin fansar wani

Matashi ya gamu da tsautsayi bayan ya kwace wayar wata mata a Kano
Mota Ta Murkushe Mai Kwacen Waya Jim Kadan Bayan Fashin. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Mene rundunar 'yan sanda ta ce a Kano?

Kakakin rundunar 'yan sanda a Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiyawa ya ce lamarin ya faru ne a daren jiya Lahadi 14 ga watan Janairu a Zoo Road yayin da ya ke kokarin tserewa.

Ya ce matashin ya fito da makami don razana matar inda ya yi nasarar kwace wayar amma ya ci karo da motar inda ta kade shi.

Wane yanayi matashin ya ke ciki a Kano?

Ya kara da cewa an kira jami'an 'yan sanda don daukar shi zuwa asibiti tare da ba shi kulawar gaggawa, cewar Leadership.

Daga bisani bayan daukar shi zuwa asibiti, Kiyawa ya ce kashin bayan matashin ya karye kuma kansa ya fashe.

Ya ce asibitin su na tunanin shigar da shi bangaren 'ICU' don ceto rayuwarsa cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Mai kwacen waya da mota ta buge a Kano ya kwanta dama

Birnin Kano na fama da 'yan daba wadanda su ka kware wurin kwacen wayar mutane a wurare da dama na birnin.

Wakilin Legit Hausa ya tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a jihar kan sanin halin da ake ciki amma bai yi martani ba.

'Yan sanda sun fitar da rahoton laifuka a Kano

A wani labarin, Rundunar 'yan sanda a Kano ta fitar da rahoton aikata laifuka bayan hukuncin Kotun Koli a jihar.

Rundunar ta ce ba a samu aikata wasu laifuka ba a jihar duk da tunanin matsalar da za a samu.

Wannan na biyo bayan yanke hukuncin Kotun Koli inda Gwamna Abba Kabir ya yi nasara kan Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.