Yankar Ƙauna: Ango Ya Gamu da Ajali, Ya Rasu a Hanyar zuwa Wurin Ɗaura Aure a Bauchi
- Allah ya karɓi rasuwar wani ango tare da abokinsa a hanyar zuwa masallacin da za a ɗaura aure yau Asabar, 14 ga watan Yuni a jihar Bauchi
- Mai shirin zama angon, Garba Mustapha ya gamu da hatsarin mota mintuna kaɗan kafin ɗaura aurensa, lamarin da ya jefa yan uwa cikin jimami
- Legit Hausa ta gano cewa an shirya ɗaura auren marigayin da amaryarsa, Khadija Adamu Sulaiman da misalin karfe 11:00 na safe a babban masallacin Magama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Wani ango da ake shirin ɗaura aurensa yau Asabar, 14 ga watan Yuni, 2027, ya gamu da ajalinsa a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Angon mai suna, Garba Mustapha ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi da safiyar yau a hanyar zuwa wurin ɗaura auren a garin Magama.

Asali: Facebook
Wani ɗan'uwan marigayin, Shamsuddeen Hasheem Zalawah ne ya tabbatar da mutuwar angon a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ango ya rasu ranar ɗaura aure a Bauchi
Ya ce Garba, wanda ke shirin angoncewa nan da ƴan sa'o'i ya gamu da hatsari tare da abokinsa, kuma an tabbatar da cewa Allah ya karɓi ransu su duka biyun.
Ɗan'uwan angon ya ce:
"Innalillahi wa inna Ilaihi rajiun, yanzun nan Allah ya yi wa ɗan uwanmu, Garba Mustapha Rasuwa. Shi ne wanda za'a ɗaura auren sa yanzu a garin Magama Gumau.
"Ya rasu ne sakamakon haɗarin mota da ya rutsa da shi da abokinsa tsakanin Gumau zuwa Magama Gumau, a kan hanyarsu ta zuwa wurin ɗaura auren.
"Allah Ya jiƙansu da rahama Ya sa Aljannah ta zama makoma, Ameeen."
Angon ya wallafa katin gayyata a shafinsa
Legit Hausa ta gano cewa an shirya ɗaura auren Garba, wanda ya kasance ɗan sanda da amaryarsa, Khadija Adamu Sulaiman da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Asabar.
A bidiyon gayyata da marigayin ya wallafa a shafinsa kwankin kaɗan da suka wuce, ya nuna za a ɗaura auren ne a babban masallacin Juma'a na Magama, ƙaramar hukumr Toro a jihar Bauchi.

Asali: Facebook
Wane hali ƴan uwan angon suka shiga?
Wannan lamari ya gigita ƴan uwansa da abokan arzikin angon, waus daga ciki sun ce gani suke yi kamar mafarki suke yi saboda sun yi magana da shi yau da safe.
Wata yar uwar mamacin, Fameenah Alqaseem ta ce:
"Ina fatan a kira ni a waya a ce mani ba da gaske ba ne, sabod ayau da safe ya hau Facebook, har magana mun yi da shi amma wai yanzu ya rasu, innalilLahi wa inna ilaihi raji'un.
"Allah mun tuba, Allah Ka gafarta wa Daddy Garba Mustapha."
Malam Isyaka Bashir ya shaidawa Legit Hausa cewa sun kaɗu da samun labarin rasuwar DPO Mustapha kuma a ranar aurensa.
"Shi ne D.P.O na Railway Station da ke unguwa mu gidansa na railway quarters duk Wanda yake mu'amala da shi ya san mutumin kirki ne.
"Mun kaɗu da jin labarin rasuwarsa, amma muna masa kyakkyawan zato, Allah Ya gafarta masa."
An kama ango kan zargin kashe amarya a Jigawa
A wani rahoton, mun kawo maku cewa ƴan sanda cafke wani sabon ango da abaokansa bisa zargin hannu a kisan amanrta kwanakin kaɗan ɗaura aure a Jigawa.
An ruwaito cewa ango da wasu abokansa uku sun shiga ɗakin amarya da niyyar tilasta mata kwanciyar aure, lamarin da ya janyo rasuwarta.
Binciken farko ya nuna cewa angon mai suna Auwal Abdulwahab mai shekara 20 ya gayyaci abokansa domin kokarin shawo kan amaryarsa.
Asali: Legit.ng