Manyan Hadurran Jirgin Sama da Suka Girgiza Duniya a Tarihi

Manyan Hadurran Jirgin Sama da Suka Girgiza Duniya a Tarihi

An samu wasu haɗurran jiragen sama a duniya waɗanda suka jawo asarar rayukan mutane masu yawa.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Haɗurran sun zama sanannu a tarihin duniya saboda yawan asarar rayuka da yanayin yadda suka auku.

Jiragen sama da dama sun gamu da hadurra
Hadurran jiragen sama da suka bar tarihi Hoto: @fiidiidata
Asali: Twitter

Haɗurran jiragen sama dai idan suka auku ana yawan samun asarar rayuka saboda munin da suke da shi, cewar rahoton Yahoonews.

Manyan haɗurran jiragen sama

Ga wasu daga cikin munanan haɗurran jiragen sama da suka auku:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Hatsarin filin jirgin Tenerife (1977)

Hatsarin ya auku ne bayan an samu karo tsakanin jirage biyu ƙirar Boeing 747 a wani filin jirgi a tsibirin Canary.

Wannan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 583, wanda shi ne hatsarin jirgin sama mafi muni a tarihi.

2. Jirgin Turkish Airlines - 981 (1974)

Hatsarin ya faru ne a Faransa sakamakon fashewar kofar ɗakin kaya wanda ya haifar da fitar iska mai ƙarfi, cewar rahoton faa.gov

Dukkan mutane 346 da ke a cikin jirgin sun rasa rayukansu a hadarin da ya faru a farkon watan Maris na 1974.

3. Jirgin Air India - 182 (1985)

Wani bam ya tarwatsa jirgin, inda dukkan fasinjoji 329 suka mutu.

Wannan shi ne harin ta’addanci mafi muni da aka taɓa kai wa wani jirgin sama.

4. Jirgin American Airlines - 191 (1979)

Hatsarin ya faru ne a tashar jirgin O’Hare a Chicago bayan inji ya fice daga jirgin yayin da yake tashi, inda mutane 273 suka mutu.

Hatsarin ya haifar da sauye-sauye masu muhimmanci wajen gyaran jirage.

5. Jirgin Saudiyya - 163 (1980)

Hatsarin jirgin Saudiyya 163 mai ɗauke da fasinjoji 301 ya auku ne bayan wuta ta tashi a cikin jirgin bayan tashinsa.

Duk da an yi saukar gaggawa, ba a samu damar fitar da fasinjoji cikin lokaci ba, wanda ya janyo mutuwar mutane 301 gaba ɗaya.

6. Jirgin Air France - 4590 (2000)

Jirgin Concorde ya faɗi bayan tashinsa daga birnin Paris saboda fashewar taya da kuma zubewar man fetur.

Mutane 109 ne suka mutu a sakamakon hatsarin wanda ya auku a shekarar 2000.

7. Jirgin Air France - 447 (2009)

Jirgin Air France 447 ya gamu da hatsarin a cikin tekun Atlantic a shekarar 2009.

Jirgin ya gamu da hatsari ne sakamakon matsalar kayan aikin gano hanya da kuskuren matuƙa, inda mutane 228 suka mutu.

8. Jirgin United Airlines - 232 (1989)

Hatsarin jirgin United Airlines ya auku ne bayan lalalcewar injin jirgin, wanda hakan ya haifar da rasa ikon sarrafa jirgin.

Matuƙan jirgin sun yi ƙoƙarin sauka da shi a Sioux City, Iowa. Duk da haka, mutane 111 ne suka mutu, amma an samu yawan waɗanda suka tsira fiye da yadda aka zata.

9. Hatsarin Mount Erebus (1979)

Wani jirgin yawon bude ido daga New Zealand ya fadi a Dutsen Erebus a Antarctica, inda dukkan mutane 257 suka mutu.

10.Jirgin ValuJet - 592 (1996)

Jirgin ya faɗi a jejin Florida Everglades sakamakon kaya da aka adana bisa kuskure a cikin jirgin. Mutane 110 ne suka mutu.

Sababbin haɗurran da suka auku

Ga jerin wasu sababbin haɗurran jiragen sama da suka auku a baya-bayan nan:

1 Hatsarin Jirgin Air India (2025)

Wani jirgin Boeing 787 wanda ya tashi daga birnin Ahmedabad zuwa London ya fadi bayan tashinsa a ranar 12 ga Yuni, inda mutane 270 suka mutu.

Jirgin Air India ya gamu da hatsari
Jirgin Air India ya fado bayan tashinsa a birnin Ahmedabad Hoto: @Aaronfoster
Asali: UGC

Fasinja daya ya tsira a mummunan hatsarin wanda ya girgiza duniya, rahoton DD News ya tabbatar.

2. Hatsarin Helikwafta a D.C (2025)

Karon da jirgin American Airlines da wani helikwafta na soji suka yi a birnin Washington D.C. ya zama mafi muni a Amurka cikin shekaru fiye da 20.

Hatsarin ya jawo asarar rayukan mutane 67.

3. Hatsarin jirgi a Koriya ta Kudu 2024

Wani jirgin Boeing 737 ya bugu da katanga yayin ƙoƙarin sauka a watan Disamba, inda mutane 179 suka rasa rayukansu.

Rahoton farko ya nuna cewa an samu fuka-fuki da jinin tsuntsaye a cikin injinan jirgin, kuma tayoyin saukar jirgi sun kasa buɗewa.

An hana jirgin sanatoci sauka

A wani labarin kuma, kun ji cewa jirgin wasu sanatoci na Najeriya ya gamu da cikas bayan an hana shi sauka a jihar Taraba.

Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu, David Jimkuta ya koka kan hana jirgin sauka a filin jirgin sama da ke Kashimbila.

David Jimkuta ya bayyana cewa matakin hana jirgin da sanatocin guda 18 suka biyo sauka a Taraba ya jawo rashin halartarsu wurin taron rabon tallafin da ya shirya a mazaɓarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng