Wutar Lantarki Ta Yi Ɓarna, Babban Jami'i a Gwamnatin Gombe da Wasu Mutum 4 Sun Rasu

Wutar Lantarki Ta Yi Ɓarna, Babban Jami'i a Gwamnatin Gombe da Wasu Mutum 4 Sun Rasu

  • Wutar lantarki ta zama sanadin mutuwar wani babban sakatare a gwamnatin jihar Gombe tare da wasu mutane huɗu a Tudun-Wadan Pantami
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da afkuwar lamarin, wanda ya faru bayan an kawo wuta mai ƙarfi da safiyar yau Asabar a birnin Gombe
  • Kwamishinan ƴan sanda ya yi alhinin mutuwar mutanen tare da tabbatar da cewa za a gudanar da bincine mai zurfi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Gombe - Wutar lantarki mai ƙarfi ta yi ajalin akalla mutane biyar yayin da wasu 13 suka jikkata a unguwar Tudun-Wadan Pantami da ke cikin birnin Gombe.

Lamarin dai ya faru ne da safiyar yau Asabar, kamar yadda Rundunar Ƴan Sandan Jihar Gombe ta tabbatar.

Wutar lantarki ta kashe mutane a Gombe
Mutum 5 sun mutu da aka kawo wutar lantarki mai karfi a birnin Gombe Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Daya daga cikin mamatan shi ne Abdullahi Kulani, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkoki na Musamman da Daidaita Yankuna ta jihar Gombe, Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Raɗaɗin wutar lantarki ya kashe mutum 5

Wannan lamari mai ban tausayi ya auku ne bayan wayewar gari, inda aka ce raɗaɗin wutar lantarki mai karfi daga wata taransufoma ya kashe mutane ba zato ba tsammani

Rahotanni sun cewa wutar ta kama mutane ne a cikin gidajensu, lamarin da ya ɗaga hankulan mazauna yankin a jihar Gombe.

DSP Buhari Abdullahi, mai magana da yawun ƴan sandan jihar Gombe, ya ce jami’ansu daga ofishin ‘yan sanda na Low-cost sun kai dauki bayan samun kiran gaggawa.

Yan sanda sun kai ɗaukin gaggawa

“Jami’anmu sun garzaya wurin da abin ya faru don tabbatar da tsaro da kuma taimakawa wajen garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa asibitoci.
“Abin takaici, mun tabbatar da rasuwar mutum biyar, yayin da mutum 13 ke fama da raunuka daban-daban," in ji shi.

Kakakin ƴan sandan ya ce sun kai gawarwakin matum uku asibitin koyarwa, guda ɗaya na asibitin kwararru, yayin da ragowar ɗayan aka ajiye ta a ɗakin ajiyar gawarwaki na Bolari

Ya ƙara da cewa an kwantar da waɗanda suka jikkata a asibitoci daban-daban a fadin jihar, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Rundunar ƴan sanda za ta yi bincike

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, CP Bello Yahaya, ya bayyana lamarin a matsayin abin “kaduwa da alhini sosai”, inda ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu.

“Muna mika sakon ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ƴan uwansu, tare da fatan warkewa cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata,” in ji shi.
Wutar lantarki ta yi ɓarna a Gombe.
Yan sanda sun yi alkawarin gudanar da bincike kan lamarin Hoto: Getty Image
Asali: Facebook

Ya kuma yi alkawarin gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin wannan haɗari, yana mai cewa:

"Za mu yi cikakken bincike don gano yadda abin ya faru da kuma daukar matakin da ya dace idan an gano akwai sakaci.”

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana lokacin da lamarin ya faru da cewa “abin firgita ne ƙwarai.”

“Mutane na ihu suna gudu. Wasu ko motsi ba su iya yi a lokacin da masu kai agaji sika iso,” in ji shi.

Za a ɗauke wuta a Gombe da jihohi 5

A wani labarin, kun ji cewa Kamfanin TCN ya sanar da cewa za a ɗauke wutar lantarki na kwanaki huɗu a jihohi shida na Arewa maso Gabashin Najeriya.

A wata sanarwar da jami'in hulda da jama'a na TCN ya fitar, kamfanin ya ce za a ɗauke wutar ne domin kafa wasu sababbin turakun lantarki.

Sanarwar da ta ce za a kafa turakun wutar lantarki masu karfin 330kV a kan layukan wuta na jihar Bauchi da ke yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262