'Kowa Ya Nemi Ƴar Garinsu': Rigima Ta Barke a Borno kan Neman Aure, an Jikkata Mutane
- Rikici ya barke a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas bayan wani matashi ya nemi auren budurwa mai shekara 17
- Matasa daga Bargu sun ki yarda da auren, sun ce ba za a bar baki su aure musu 'yan mata ba, lamarin da ya rikide zuwa fada
- Bayan da rikicin ya ci gaba a kasuwar Bargu, an jikkata mutane da dama, an kona babur, jami’an 'yan sanda sun dawo da zaman lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Shani, Borno - Wani lamari da ya shafi neman aure ya rikice zuwa tashin hankali a jihar Borno da ke Arewacin Najeriya.
Majiyoyi sun ce tayin neman aure da bai yi kyau ba ya janyo rikicin kabilanci a karamar hukumar Shani ta jihar Borno.

Asali: Original
An jikkata mutane kan neman aure a Borno
Rahoton Zagazola Makama ya ce mutane da dama sun jikkata, lamarin da ya tilasta 'yan sanda suka shiga tsakani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyin sun shaida cewa rikicin ya faru a ranar 11 ga Yuni, 2025 a garin Bargu da ke karamar hukumar Shani.
Rikicin ya samo asali ne bayan wani matashi, Mamaru daga Kubo, tare da abokansa, sun ziyarci kauyen Bargu domin neman auren Babaliya Hassan.
A cewar majiyoyi, Babaliya ta shimfida tabarma a kofar gidan mahaifinta don murnar abin alheri da ke tafe da su.
Amma wasu matasa daga Bargu sun hana, suna cewa “baki ba su da hurumin auren ‘yan yankinsu.”
Wannan adawa ta rikide zuwa fada, wanda ya sa Babaliya ta koma cikin gida yayin da Mamaru da abokansa suka tafi.
An dan samu kwanciyar hankali, amma lokacin da suka dawo daukar tabarma, Babaliya cikin bacin rai ta bugi Muhammad Isa da tabarya, ta jikkata shi sosai.

Asali: Twitter
Rigimar neman aure: Yan sanda sun shiga tsakani
Wani mutum mai suna Shuaibu Ali ya sami rauni kadan a cikin hargitsin, washegari, kasuwar Bargu na ci, rikicin ya sake tsananta.
Matasa daga Kubo sun kai harin ramuwar gayya bisa labarin jikkatar abokansu, inda suka dira Bargu a kan babura.
Yayin rikicin, matasan Bargu sun farmaki wani mai suna Friday Lado tare da kona babur dinsa.
Sannan sun kama karin babura guda shida mallakin matasan Kubo. Rikicin ya kuma jikkata wata mata, Rukayya Buba, da ta fada tsakaninsu.
An kara samun bayani cewa rundunar ‘yan sanda ta Borno ta aike da tawagar kwararru, inda suka kwantar da tarzoma tare da daukar wadanda jikkata zuwa asibiti.
An sallami wadanda suka jikkata bayan sun warke, sannan aka mika baburan da aka kama zuwa ofishin ‘yan sanda na Shani domin tsarewa.
An rasa rai kan budurwa a Niger
Kun ji cewa wani matashi mai shekaru 25, Usman Mohammed, ya mutu bayan an daba masa wuka a rikici da ya faru a jihar Niger.
An ce Usman ya ziyarci budurwarsa Halima a Barikin-Sale, inda wasu matasa uku suka nemi lalata da ita da kudi, amma ta ki amincewa.
Daya daga cikin matasan ya daba wa Usman wuka a bayansa, daga bisani ya mutu a asibiti yayin da aka kai shi domin ba shi kulawa.
Asali: Legit.ng