Yadda Inyamurai Musulmai Ke Shan Wahalar Neman Aure a Yankunansu Na Kudancin Najeriya

Yadda Inyamurai Musulmai Ke Shan Wahalar Neman Aure a Yankunansu Na Kudancin Najeriya

  • Babban liman a jihar Imo, Sheikh Suleiman Njoku, ya bayyana kalubalen da musulmai 'yan kabilar Igbo ke fuskanta a yankin Kudu maso Gabas
  • Malamin addinin musuluncin ya bayyana yadda ta'addanci da 'yan batun 'yan bindiga a Arewa ke bata sunan Muslunci a idon kabilun Igbo, wanda hakan ke jawo wariya da rashin fahimta
  • Duk da kalubalen da ake fuskanta, Sheikh Njoku ya lura da yadda addinin Musulunci ke bunkasa a jihar Imo, ya kuma yi kira da a tallafawa ilmin addinin Musulunci a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Imo - Babban malamin addinin Islama a jihar Imo, Sheik Suleiman Njoku, ya bayyana irin kalubalen da musulmai ‘yan kabilar Igbo ke fuskanta a yankin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Zargin cushe a kasafi: Tinubu ya dira kan Sanata Ningi, ya kwance masa zani a kasuwa

Yankin Kudu maso Gabas dai galibin mazauna yankin 'yan kabilar Igbo ne da suka jima da karbar addinin Kirista baya ga addinin gargajiya.

Da yake zantawa da jaridar Punch, malamin ya yi tsokaci ga yadda Musulmai da suke yankin ke fama da kalubale na nuna wariya da kyama.

Ba a son auren Musulmai a kabilar Igbo
'Yan Igbo ba sa son auren Musulmi, inji malamin Imo | Hoto: @haruna_braimoh
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ya bayyana yadda sauran addinai a yankin, kamar na gargajiya da na Kirista suka cudanya da kabilun yankin har suka zama kamar al'ada daya.

Boko Haram da 'yan bindiga sun bata Arewa

A bayanansa, ya ce kadan daga dalilan da ke jawo ake yiwa Musulmai kallon saniyar ware a yankin ba komai bane face yadda 'yan ta'adda a Arewa suka jawo bacin suna ga addinin.

A cewarsa, yadda Boko Haram ke alakanta kanta da addini babban kalubale ne da jawo ake yiwa addinin Islama kallon addinin ta'addanci.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan farmaki Zamfara, sun halaka masu azumi da dama

Hakazalika, 'yan bindigan da ke sace mutane kuma suna ikrarin su Musulmai ne shi ma ya shafa bakin fenti ga addinin na Islama.

Igba ba sa son auren Musulmi

Da yake karin haske, ya bayyana cewa, har yanzu akwai tsaiko na yadda 'yan kabilar ta Igbo ke kyamar auren Musulmi.

Haka nan, ya ce sukan yi tsoratarwa ga 'yan uwansu ga shiga addinin na Islama ko ma dauko aure daga gidan Musulmai.

A kalamansa:

"'Yan kabilar Igbo ba sa son auren Musulmi, don haka suke hana duk wanda ke son auren Musulmi yin hakan."

Addinin Islama na kara habaka a Kudu

A bangare guda, Sheikh Njoku ya ce, addinin Islama na ci gaba da samun karbuwa a jihar Imo duk da matsalolin da ake fuskanta.

Ya kuma bayyana wasu daga kalubalen da ake fuskanta, ciki har da karancin ilimi da kayayyaki yada ilimin addinin Islama a yankin.

Kara karanta wannan

Tunji-Ojo: Badakalar Betta Edu da wasu zarge-zarge 2 da ake yi wa ministan Tinubu

Shehin malamin wanda kuma lauya ne ya ce, akwai bukatar kafa makarantun Arabiyya da ke koyar da ilimin addini cikin sauki.

Daga karshe, ya musanta bayanan da ake yadawa cewa, wai 'yan kabilar Igbo na shiga addinin Islama ne saboda kudi ba don Allah ba.

Dalilin da yasa Peter Obi ke rabar Musulmai

A wani labarin, kun ji yadda Tanko Yunusa ya bayyana gaskiyar dalilin da yasa Peter ke shiga Musulmai a 'yan kwanakin nan.

A cewarsa, ba sabon abu bane ganin dan takarar shugaban kasan na 2023 yana yin buda-baki da Musulmai.

Hakazalika, ya ce Obi na yawan cudanya da Musulmai, inda a sadda yake gwamna ya taba shan ruwa da Musulmai a Onitsha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel