Niger: Matashi Ya Rasa Ransa yayin Artabu kan Budurwa, an Gano Sanadin Rigimar

Niger: Matashi Ya Rasa Ransa yayin Artabu kan Budurwa, an Gano Sanadin Rigimar

  • Wani saurayi mai shekaru 25, Usman Mohammed, ya mutu bayan an daba masa wuka a rikici da ya faru a jihar Niger
  • Usman ya ziyarci budurwarsa Halima a Barikin-Sale, inda wasu matasa uku suka nemi lalata da ita da kudi, ta ki amincewa
  • Daya daga cikin matasan ya daba wa Usman wuka a bayansa, daga bisani ya mutu a asibiti yayin da aka kai shi domin ba shi kulawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Wani matashi dan shekara 25 ya rasa ransa sanadin rigima kan budurwa a jihar Niger da ke Arewacin Najeriya.

An ce matashin mai suna Usman Mohammed ya rasa ransa bayan an daba masa wuka a rikici da ya shafi budurwarsa a Barikin-Sale, Minna.

An kashe matashi kan budurwa a Najeriya
Matashi ya rasa ransa a Niger yayin artabu kan budurwa. Hoto: Legit.
Asali: Original

An kashe matashi saboda budurwa a Niger

Zagazola Makama ya gano cewa lamarin ya faru ne da daddaren Litinin 9 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya faru lokacin da Usman ya ziyarci budurwarsa Halima Usman a 'Deeper Life Upper Base', Barikin-Sale.

Yayin da suke zaune suna hira a waje, wasu matasa uku da aka bayyana da sunaye Barafi, Ayya da wani wanda ba a san shi ba sun iso.

Musabbabin cakawa matashi wuƙa saboda budurwa

Shaidu sun bayyana cewa matasan sun ba Halima N5,000 domin ta fita da su, amma ta ki amincewa da bukatarsu.

Lamarin ya rikide zuwa tashin hankali, inda daya daga cikinsu ya ciro wuka ya daba wa Usman wanda shi ne saurayin budurwar wuka a bayansa har sai da ya fadi.

An tabbatar da cewa bayan caka masa wuka ne aka kawo ɗauki wanda hakan ya tilasta kai shi asibiti da gaggawa.

An rasa rai a Niger kan rigimar budurwa
Matashi ya mutu sanadin fada kan budurwa. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Yadda Usman ya mutu a asibiti a Niger

An garzaya da Usman zuwa asibitin gwamnati na Minna domin ba shi agajin gaggawa, amma daga baya ya rasu a asibiti da misalin karfe 2:30 na safiya Talata.

An kama daya daga cikin wadanda ake zargi, Ahmed Mohammed yayin da aka fara farautar sauran biyun da suka tsere daga wurin.

‘Yan sanda sun ziyarci wurin da abin ya faru, inda suka dauki hoton mamacin kafin a kai gawarsa dakin ajiye gawa don yin bincike.

An cafke wani da ake zargi kan lamarin

Ahmed Mohammed yana hannun hukuma, yayin da ake ci gaba da kokarin kamo sauran wadanda ake zargi da hannu a harin.

Ana ci gaba da bincike kan lamarin domin gano musabbabin tashin hankalin da ya janyo mutuwar saurayin a wannan yanayi da ake ciki.

An kashe matashi kan budurwa a Adamawa

Kun ji cewa wani matashi ya rasa ransa yayin da daya ke kwance rai a hannun Allah bayan rikici kan wata budurwa yayin bikin sallah a Adamawa.

Rikicin ya barke ne tsakanin matasa biyu, Idrisu Nuhu mai shekara 18 da Ahmadu Lawali mai shekara 16, inda suka kai wa juna farmaki da adda.

Idrisu ya samu mummunan rauni a kansa, yayin da Ahmadu ya gamu da rauni a wuyansa, likita ya tabbatar da mutuwar Idrisu a asibiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.