Manyan kurakurai 5 da maza ke tafkawa wajen neman aure

Manyan kurakurai 5 da maza ke tafkawa wajen neman aure

Aure wani ginshiki ne na jin dadin duniya, sannan kuma abune da kowa ke burin yi a rayuwa. Bugu da kari, aure kan karawa masu yenta kima da daraja a idanun duniya.

Sai dai yin auren ba shine ba abu mafi muhimmanci shine mallakar abokin zama na gari. Kuma akan samu zaman lafiya ne a gidaaure idan har aka shimfada soyayya kan tubalin gaski, yarda da kuma amana.

Mazaje da dama sukan yi kuskure wajen neman matan aure. Don haka mukayi amfani da wannan dama wajen zayyano wasu manyan kura-kurai 5 da maza kan yi a wajen neman aurensu.

Gasu kamar haka:

1. Rashin neman mai kyaun dabi’a: Babban abin da ya kamata ka fi mayar da hankali a kai shi ne, neman mace mai kyawawan dabi’u, wacce za ka iya zama da ita don Allah, wacce za ta kai ka tudun-mun-tsira, ba wacce za ta kama hannunka ku tsunduma cikin wuta ba.

2. Karancin wayewa: Sau tari wasu mazan sukan gabaci mace, su rika nuna tsanin wayewarsu ta zamani. A ganinsu wannan ne dalilin da zai sa su karbu wajen Mace. Sannan a hakan kuma saboda rashin wayewar tasu, babu abin da za su fi mayar da hankali a kai illah neman wacce wai take da wayewar Zamani.

3. Karya: Karya tana daga cikin irin abubuwan da ke zubar da mutuncin mutum wajen wacce zai aura. Ka ga matashi yana yi wa yarinya karya, ai shi mai arziki ne, idan ta aure shi ta huta. Ya rika karbar aron abubuwan duniya don ya rude ta. Wannan shi ne mataki na karshe a rashin Wayewa, da fatar masu irin wannan halin za su fadaka su daina.

KU KARANTA KUMA: Rashawa: Buhari yace za’a kirkira kotuna na musamman, ya gargadi barayin gwamnati

4. Kazanta: Tana daga cikin abubuwan dake sa ka rasa kima a wajen Mace saboda gaskiya mata na da tsabta yadda ya kamata, saboda haka ba sa son namiji kazami. Abin alfaharin Mace ne ta nuna ka a gaban kawayenta ka yi wanka mai kyau, ka hadu.

5. Rowa: Dukkan mace tana son kyauta, ya zamana hannun saurayi a bude yake. Duk da ba a dora sharadin aure kan yin kyautar kudi ba, amma Manzon Allah (saw) ya fadi cewa, “Zuciya tana jawuwa bisa son wanda yake kyautata mata, sannan tana kin wanda ya munana mata”. Kenan ashe kyauta za ta iya taka muhimmiyar rawa a wajen neman aure.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng