Farashin Danyen Mai: Najeriya Ta Fara Cin Ribar Yakin Iran da Isra'ila

Farashin Danyen Mai: Najeriya Ta Fara Cin Ribar Yakin Iran da Isra'ila

  • Sabon fada da ya kaure tsakanin Isra’ila da Iran ya haifar da tashin farashin gangar danyen mai zuwa sama da $75
  • Farashin ya haura hasashen da aka gina kasafin kudin Najeriya na 2025 wanda aka gina shi a kan kudin ganga zai kasance $75
  • Tashin farashin na iya taimakawa wajen cike gibin kasafin kudin da kara darajar Naira a kasuwar canjin kudi ta duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sabon rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da Iran ya haddasa tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, inda ganga ta haura $75

Bincike ya nuna cewa sabon farashin ya haura hasashen da aka gina yadda kudin danyen mai zai kasance domin samun kudin da za a aiwatar da kasafin kudi na shekarar 2025.

Bola Tinubu yayin gabatar da kasafin kudin Najeriya
Bola Tinubu yayin gabatar da kasafin kudin Najeriya a majalisa. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Rahotan Business Day ya nuna cewa farashin danyen mai na Brent ya tashi da sama da 9% inda ake sayar da ganga daya a $75.15, mafi tsada tun watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tasirin tashin farashin kan kasafin kudin Najeriya

Kasafin kudin 2025 na Najeriya ya ginu ne a kan farashin gangar danyen mai zai kasance a kan $75.

Sai dai tashin farashin da aka samu samu yanzu ya nuna yiwuwar cike gibin kasafi da kasar ke fama da shi sakamakon farashin mai da ya dade yana tangal-tangal a kan $60.

Mai nau’in Bonny Light da Najeriya ke fitarwa kuma ke da farashi mafi tsada da Brent, ana sayar da gangar shi shi a kusan $78.6, wanda ke nuna wani karin riba a kudin shiga.

Hakan na iya rage bukatar gwamnati ta cin bashi, da kuma tallafa wa aiwatar da ayyuka ba tare da kara haraji ko shiga matsalar kudi ba.

Tasirin tashin farashin mai kan Naira

Tattalin arzikin Najeriya na samun fiye da kashi 90 cikin 100 na kudin waje daga danyen mai, don haka karuwar farashin mai na iya shigowa da karin daloli cikin tattalin arziki.

Ana ganin karin na iya rage matsin lamba kan Naira, wanda yanzu ake canzawa a sama da N1,600 kan kowanne Dala, fiye da darajar da kasafin kudin 2025 ya kayyade wato N1,400.

Karuwar kudin mai na iya kara yawan kudin waje da ke samu da kuma kara tallafawa kasuwar musayar kudi.

Yakin Iran da Isra'ila ya shafi farashin mai a duniya
Yakin Iran da Isra'ila ya jawo tashin farashin danyen mai a duniya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Farashin danyen mai zai cigaba da tashi?

Duk da alfanun da ke tattare da tashin farashin, masana sun ja hankali cewa lamarin ka iya zama na dan lokaci, duba da yadda rikicin Gabas ta Tsakiya ke iya daukar sabon salo.

Tarihin kasuwar mai ya nuna cewa matsin lamba na siyasa na iya janyo rikice-rikice da sauyin farashi cikin gaggawa, wanda ke sa kasuwanni cikin fargaba da rashin tabbas.

Rahoton Daily Post ya nuna cewa duk da da tashin farashin, za a iya fuskantar karin kudin fetur a gidajen mai a Najeriya.

Iran ta harba jiragen yaki 100 Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Iran ta ce za ta kai zafafan hare hare kan Isra'ila bayan harin da aka kai mata.

A karon farko, Iran ta kai harin ramakon gayya da jiragen yaki marasa matuka guda 100 zuwa kasar Isra'ila.

Sai dai Legit Hausa ta rahoto cewa kasar Isra'ila ta ce ba za ta tsaya ta zuba ido ba Iran ta ci karenta babu babbaka a kanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng