Ma’aikatan Lafiya 1,500 Sun Shiga tsaka Mai Wuya, An Hana Su Albashin Watanni 20
- Fiye da ma’aikata 1,500 na hukumar lafiya EHCON sun shafe watanni 20 babu albashi sakamakon dokar gwamnati
- Wani umarnin gwamnatin tarayya a shekarar 2023 da ya hana biyan kuɗi ga wasu hukumomi ciki har da EHCON
- A 2024, gwamnati ta cire EHCON daga jerin hukumomin da za su ci gaba da samun kuɗi daga cikin kasafin Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fiye da ma’aikatan lafiya 1,500 da ke ƙarƙashin hukumar lafiyar muhalli ta kasa (EHCON) sun shiga matsalar rashin albashi.
Wadannan ma'aikata sun shafe tsawon watanni 20 ba su samu damar karbar albashin ayyukansu ba daga Gwamnatin Tarayya.

Asali: Facebook
Wannan matsala ta samo asali ne daga wani umurni da Gwamnati ta bayar a shekarar 2023 da ya hana biyan kuɗi ga wasu hukumomi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ta ce lokaci ya yi da hukumomin za su ci gashin kansu tare da cigaba da gudanar da dawainiyar da za ta taso masu.
An dorawa hukumar lafiya kula da kanta
Business Day ta ruwaito a shekarar 2023, tsohon daraktan ofishin kasafin kuɗi na ƙasa, Ben Akabueze, ya sanya hannu kan rwasiƙa da ta ayyana cewa wasu hukumomi za su daina samun kasafi daga gwamnati.
A cikin wasiƙar, an bayyana cewa:
"Kwamitin shugaban ƙasa kan albashi ya amince da dakatar da bayar da kasafi ga wasu hukumomi daga 31 ga Disamba, 2026.”

Asali: Facebook
Wani rahoto ya tabbatar da cewa wasu daga cikin hukumomi 30 da abin ya shafa za su ci gaba da samun kuɗi har zuwa 2026, yayin da sauran za a cire su daga tsarin daga Disamba 2024.
Gwamnati ta katse kula da wasu hukumominta
A shekarar 2024, Ofishin Kasafin Kuɗi ya fitar da jerin cibiyoyi 26 da za a fara katse musu kasafi daga gwamnati.
Gwamnati ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen adana Naira biliyan 27.72 a a ƙasar nan.
EHCON na daga cikin waɗanda an cire daga jerin hukumomin da za su ci gaba da samun kuɗi, abin da ya janyo gibin albashi da kuɗin gudanarwa a hukumar.
A shekarar 2024, Ministan Ƙananan Harkokin Lafiya, Tunji Alausa, ya roƙi gwamnati da a cire hukumomin lafiya daga jerin da za a yanke musu tallafi.
Wannan ya sa gwamnati ta fitar da sama da Naira biliyan shida domin biyan ma’aikatan wasu hukumomin lafiya guda 13 da aka keɓe.
A ranar 30 ga Afrilu, 2025, Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya aika wasiƙa zuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana roƙon a sassauta wa ma’aikatan EHCON.
Gwamnati ta kara albashin likitoci
A baya, kun ji cewa gwamnan Ebonyi, Francis Ogbonna Nwifuru, ya ce zai fara biyan sabon albashin N500,000 ga sababbin likitocin da aka ɗauka aiki a cibiyoyin lafiya na jihar.
Gwamnatin jihar ta ce ta kashe fiye da ₦10bn wajen gyara asibitoci, sayen kayan aiki da samar da magunguna masu rahusa, tare da ɗaukar ma’aikata 195 a fannin lafiya.
Gwamna Nwifuru ya kaddamar da tsarin rabon kayan aiki na zamani kamar gadaje, matasai da ma na’urar auna lafiyar marassa lafiya tare da tallafin magunguna ga asibitoci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng