NEMA: Sama da Gonaki 14,000 ne Ambaliyar Ruwa Tayi Awon Gaba da Su a Kano

NEMA: Sama da Gonaki 14,000 ne Ambaliyar Ruwa Tayi Awon Gaba da Su a Kano

  • Hukumar bayar da agajin gaggawa, NEMA, ta sanar da lalacewar gonaki sama da 14,000 a fadin jihar Kano sakamakon ambaliyar ruwa
  • Lamarin ya shafa gonakin manoma a kananan hukumomin Warawa, Wudil, Bebeji, Rano, da Dawakin Kudu
  • Darakta Janar na NEMA, Mustapha Ahmed Habib, ya ziyarci yankunan da lamarin ya shafa kuma yace za a kai musu kayan rage radadi da tallafi

Kano - Hukumar bayar da agajin gaggawa, NEMA, ta ce a kalla gonaki 14,496 ne ambaliyar ruwa ta lalata a kananan hukumomi biyar na fadin jihar Kano.

Darakta Janar na Hukumar NEMA, Mustapha Ahmed Habib, ya bayyana hakan ga manema labarai yayin wani rangadin tantancewa da ya kai wasu al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin Warawa da Wudil na jihar.

Ambaliyar ruwa
NEMA: Sama da Gonaki 14,000 ne Ambaliyar Ruwa Tayi Awon Gaba da Su a Kano. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa, shugaban ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumar da ta gudanar da tantance irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi, sannan ya yi alkawarin tallafa wa wadanda abin ya shafa da kayayyakin rage radadi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar Bana SSCE 2022

A cewarsa, kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Warawa, Wudil, Bebeji, Rano, da Dawakin Kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wasu daga cikin al’ummomin da lamarin ya shafa sun hada da gonaki a Warawa Gishiri Wuya 1,113, Larabar Gadon Sarki gonaki 1,135, gonaki na Wudil 4,808, gonakin Bebeji 1,405, gonaki a Rano 260, da karamar hukumar Dawakin Kudu mai gonaki 5,775 duk ambaliyar ta tafi dasu.
“Don haka ne muka zo nan tare da daukacin tawagar domin tantancewa. Amma abin takaici saboda yanayin hanyar a wasu yankunan da abin ya shafa a karamar hukumar Warawa, ba mu iya shiga gonakin ba, saboda motocin mu sun makale. Sai da muka koma wasu wurare a karamar hukumar Wudil."

- Yace.

Ya kara da cewa za a hada rahoton tantancewar sannan a mika shi ga ma’aikatar jin kai da kula da ibtila'i da ci gaban al’umma domin mikawa shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Allah Ya Yiwa Sarkin Lokoja, Dr Muhammadu Maikarfi, Rasuwa

Ya ce yayin da hukumar za ta samar da kayan agaji ga wadanda abin ya shafa, gwamnatin tarayya za ta sa hannu cikin gaggawa tare da tallafa wa manoma ta yadda za su iya dawo da asarar da suka yi.

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da Alhaji Yahaya, Manomi a garin Tiga, ya bayyana irin asarar da yayi a wannan daminar.

"A gaskiya na tafka babbar asara a daminar bana saboda na narka kudina fiye da yadda na saba a noma. Amma cikin ikon Allah sai ruwan sama ya wanke gonar tas yayi awon gaba da amfanin da ya fito.
"Dalilina na kara yawan noman da nake yi shi yadda na ga kullum farashin kayan abinci na kara hauhawa yake
"Da abinda na noma nake ciyar da matana 3 da 'ya'ya 18 da nake da su. Muna fatan gwamnati zata dube mu tare da rage mana radadi kuma Allah ya sa mana hakuri da imanin wannan kaddarar."

Kara karanta wannan

An gano wata maboyar 'yan bindiga a Arewa, an fatattaki tsageru, an ceto mutanen da aka sace

- Manomin yace

Katsina: Yadda Rugugin Ruwan Kankara Ya Lalata Gonakin Jama'a

A wani labari na daban, wata gagarumar ruwan kankara ya lalata gonaki da gidajen jama'a a yankunan Dutsen-Kura/Kanya da Gozaki a karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Malam Abdullahi Gozaki, wani mazaunin garin Gozaki ya sanar da Daily Trust cewa babu wani mutum daya da ya taba fuskantar irin wannan lamarin a yankin.

Yace gonakinsu, rufin gidaje da gilasan motoci duk suna lalace sakamakon ruwan kankarar da aka yi na tsawon mintuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel