Tinubu Ya Gwangwaje Farfesa Jega da Babban Mukami a Gwamnatinsa

Tinubu Ya Gwangwaje Farfesa Jega da Babban Mukami a Gwamnatinsa

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba Farfesa Attahiru Jega muƙami a gwamnatinsa wanda zai yi aiki a bangaren kiwon dabbobi
  • An bayyana nadin nasa a wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X a yau Juma'a
  • A cikin sanarwar, Onanuga ya ce an nada Jega domin ya zama mai ba da shawara kan kiwon dabbobi da inganta harkar a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan Farfesa Jega ya jagoranci kwamitin inganta harkokin kiwo wanda Tinubu ya nada shi a kwanakin baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gwangwaje Farfesa Attahiru Jega da muƙami a gwamnatinsa.

Bola Tinubu ya ba tsohon shugaban hukumar zabe ta INEC muƙamin hadiminsa a bangaren kiwon dabbobi.

Kara karanta wannan

An fara cike fom domin samun tallafin noman Naira miliyan 1 na Sanata Barau

Tinubu ya ba Attahiru Jega muƙamin mai ba sha shawara
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya gwangwaje Farfesa Attahiru Jega da mukami. Hoto: @aonanuga1956.
Asali: Twitter

Kwamitin da Jega ya jagoranta a gwamnatin Tinubu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X a yau Juma'a 7 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya ce yana fatan nadin zai kawo ci gaba a fannin kiwo da kuma karfafa kokarin bunkasa kasa.

Jega, tsohon shugaban Jami’ar Bayero, ya jagoranci Kwamitin Kiwo na Shugaban Kasa tare da gwamnatin Tinubu.

Kwamitin ya gabatar da shawarwari na inganta kiwo, ciki har da kirkiro Ma’aikatar raya dabbob, wacce yanzu ke da minista.

Jega, mai shekara 68, mamba ne a Majalisar Kula da Zabe ta Duniya kuma Shugaban Majalisar Jami'ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano.

Ya shugabanci Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC daga 2010 zuwa 2015 bayan nasarar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Jega ya samu mukami a gwamnatin Tinubu
Farfesa Attahiru Jega ya samu mukamin hadimi ga Bola Tinubu. Hoto: @aonanuga1956.
Asali: Twitter

Wane mukami Tinubu ya ba Farfesa Jega?

A cikin sanarwar, Onanuga ya ce Jega zai zama mai ba da shawara a bangaren kiwon dabbobi da kuma inganta sha'anin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da umarnin daukan matasa aiki a dukkan jihohin Najeriya

Sanarwar ta ce:

"Shugaba Bola Tinubu ya nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin mai ba da shawara kuma mai kula da inganta kiwon dabbobi na shugaban kasa."

Karanta wasu labarai game da Jega:

Farfesa Jega ya gano matsaloli a dimukradiyya

A baya, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC ya taɓo batun juyin mulkin da ake samu a musamman yankin Afirika ta Yamma.

Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa dimukuraɗiyya na ja da baya a yankin sakamakon riƙon sakainar kashi da shugabanni suke yi wa amanar da aka ba su.

Kara karanta wannan

Ana batun cin zarafin Sanata, Remi Tinubu ta bukaci karin wakilcin mata a majalisa

Tsohon shugaban INEC ya yi kira da a gaggauta kawo sababbin tsare-tsare waɗanda za su tabbatar da cewa zaɓe ya yi daidai da ra'ayin jama'a, babu magudi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng