Zamfara: Ƴan Bindiga Sun Shammaci Masu Sallah a Masallaci, Sun Kwashe Al'umma
- 'Yan bindiga sun kai hari cikin masallaci a Unguwar Galadunci da ke Anka a jihar Zamfara a farkon daminar shekarar nan
- Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin da dare yayin da ake tsuga ruwan sama a yankin da ke kuka da miyagu
- Yan bindigar sun sace wasu daga cikin masu ibada yayin sallar Ishai, inda wasu suka jikkata kamar yadda aka tabbatar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Anka, Zamfara - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kuma kai wani hari a jihar Zamfara.
Majiyoyi sun ce maharan sun kwashe masallata a ciki masallaci a lokacin da ake tsaka da tsuga ruwan sama.

Asali: Original
Zamfara: Yan bindiga sun kai hari a masallaci
Sanarwar da shafin Bakatsine mai sharhi kan lamuran tsaro ya tabbatar da haka a manhajar X a yau Asabar 24 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce harin ya zo ne a daidai lokacin da miyagu ke ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Sanarwar ta ce:
"A daren jiya lokacin sallar Isha, 'yan bindiga sun farmaki wani masallaci a Unguwar Galadunci, karamar hukumar Anka, Jihar Zamfara.
"Sun sace wasu daga cikin masu ibada, yayin da wasu kuma suka jikkata.
"Wannan hari na daga cikin munanan hare-haren da ke ci gaba da addabar al'ummomin Arewa maso Yamma."

Asali: Facebook
Yadda yan bindiga suka sace masallata a Zamfara
An tabbatar da cewa hakan ya faru yayin da Musulmai ke cikin masallacin suna jiran sallah isha'i yayin da ake ruwan sama.
Yan bindigar sun yi nasarar tafiya da mutane da dama dake cikin masallacin wadanda ke jiran sallar Ishai kafin komawa gidajensu.
Hakan ya afku duk da yanayi na ruwa da ake ta yi babu kakkautawa a lokacin wanda bai hana su zuwa ciki garin ba.
Legit Hausa ta yi magana da matashi a Zamfara
Wani Ahmad Abdullahi daga Anka ta tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa yadda lamarin ya faru da ya daga hankulan mutanen yankin.
Abdullahi ya nuna damuwa game da harin inda ya ce an kwashe mutane da dama da ke masallacin da dare.
A karshe, ya yi addu'ar ubangiji ya kubutar da wadanda aka sace yayin harin da kuma rokon Allah ya kawo zaman lafiya a jihar da ma Najeriya baki daya.
Ya ce:
"Allah ya yi masu mafita ta alheri, ya dawo da su cikin iyalansu lafiya, ya ba mu zaman lafiya mai dorewa a jihar Zamfara da kasa baki daya, Amin."
Yan bindiga sun sace limami a Sokoto
Kun ji cewa yan bindiga sun afka wa wani masallaci a garin Bushe na ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka sace akalla mutum 10, ciki har da liman.
Jami'an ’yan sandan Sokoto sun tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa ana kokarin ceto mutanen da 'yan bindigar suka sace.
Wani dan majalisar dokokin jihar ya yabawa sojoji bisa hana ’yan bindigar yin garkuwa da karin mutane bayan sun kai mummunan harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng