Zamfara: Ƴan Bindiga Sun Shammaci Masallata a Ranar Sallah, Sun Yi Kisa
- 'Yan bindiga sun kai wani mummunan farmaki a masallacin Dole Moriki da ke Zurmi a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya
- Rahotanni sun tabbatar da cewa yayin harin, an harbe mutum daya da kuma jikkata wasu biyu yayin sallar Isha
- Wani majiya ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare lokacin da mutanen ke tsaka da ibada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Wasu yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a jihar Zamfara a ranar sallah.
An ce miyagun sun farmaki masallata ne da ke sallar isha a karamar hukumar Zurmi da ke jihar a Arewacin Najeriya.

Asali: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ya ce aƙalla mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu biyu suka jikkata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muggan hare-hare da yan bindiga ke kaiwa
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohi da ne fama da hare-haren yan bindiga wanda ya daidaita al'ummomi da dama musamman yankunan karkara.
Kai hari kan masallata ba sabon abu ba ne musamman a Arewacin Najeriya duba da yadda miyagu ke cin karensu babu babbaka.
A kwanakin baya ma, maharan sun kai wani mummunan hari a unguwar Galadunci a karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.
Maharan sun kai hari cikin masallaci a unguwar da ke karamar hukumar a jihar a farkon daminar shekarar nan da muke ciki.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin da dare yayin da ake tsuga ruwan sama a yankin da ke kuka da miyagu.
Yan bindigar sun sace wasu daga cikin masu ibada yayin sallar Ishai, inda wasu suka jikkata kamar yadda aka tabbatar.
Zamfara: Yadda yan bindiga suka farmaki masallata
Majiyoyi suka ce an kai harin ne a masallacin Dole Moriki da ke karamar hukumar Zurmi a jihar.
Majiyoyin leƙen asiri sun shaida cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare a ranar Asabar 7 ga watan Yunin 2025.
"Mutum ɗaya ya mutu a wurin, yayin da wasu biyu suka jikkata bayan da 'yan bindigar suka bude wuta yayin sallar Isha."
- Cewar wata sanarwa

Asali: Original
Matakin da jami'an tsaro suka ɗauka a Zamfara
Jami'an tsaro sun iso wurin don fuskantar 'yan bindigar da kuma tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankin.
An kai waɗanda suka jikkata da mamacin zuwa Asibitin Gaba ɗaya na Moriki, inda ake kula da marasa lafiyar yanzu.
An mika gawar mamacin ga 'yan uwansa domin a yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin Musulunci.
Shugabannin Fulani sun bukaci sulhu da hukumomi
Kun ji cewa Shugabannin Fulani a Zamfara sun koka kan yadda ake nuna musu wariya da zalunci, sun ce ba su duka ba ne ‘yan ta’adda ba.
A wani taron wayar da kai a Gusau, shugabannin Fulani sun bayyana damuwarsu, suka ce rashin adalci ke tura matasa shiga ta’addanci.
Wasu fitattun shugabannin miyagun ‘yan bindiga sun bayyana shirin su na mika wuya matukar gwamnati ta ba su tabbacin tsaro.
Asali: Legit.ng