Fada a kan budurwa: An kashe mutum 1, jama'a masu yawa sun jigata
- Rikici ya barke tsakanin wasu matasa biyu a garin Jalingo duk a kan budurwa
- Daga bisani rikicin ya sauya salo inda ya koma na addini tsakanin kiristoci da musulmi
- gaggawar zuwan jami'an tsaro yankin yasa aka rasa rai daya kuma wasu suka jagata
Wani mugun fada da aka yi a kan soyayyar budurwa ta sa an kashe mutum daya a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito yadda aka yi fadan a yankin gidan ruwa na Jalingo wanda ya janyo asarar kadarorin miliyoyin naira.
An gano cewa fadan ya koma na addini saboda daya daga cikin samarin ya yi hayar 'yan daba domin tada hankula. Dayan saurayin kuwa ya kira abokansa ne domin su taimaka masa samun nasara.
KU KARANTA: Kisan manoma 40: Duniya bata siyarwa da Najeriya makamai, an bar mu hannun 'yan ta'adda, Lai Mohammed
Amma kuma lamarin ya lafa bayan da jami'an tsaro suka isa yankin.
Wani dan kasuwa wanda ya kware a aikin biredi mai suna Salihu Sale, ya ce "Lamarin ya fara a kwanaki hudu da suka gabata bayan karamin rikici ya barke. Ya zama gagarumin fada tsakanin matasan yankuna biyu a kan budurwa.
"Daga baya ya koma rikicin tsakanin Kiristoci da Musulmi matasa. Sun dinga balle tagogi da kofofi amma kuma daga bisani jami'an tsaro sun isa inda suka shawo kan lamarin."
KU KARANTA: Kasar Saudi Arabia ta magantu a kan kisan manoma 40 a Borno
Wani ganau ba jiyau ba mai suna Ezekiel Ali ya ce: "Duk da ni ba kwararre bane, daga abinda na gani shine, an harbi daya daga ciki kuma na ga ramukan harsashi a jikinsa."
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmed Azare, wanda ya ziyarci yankin ya kushe lamarin kuma ya ce mutum daya tak aka kashe.
Azare ya bayyana cewa an kama wasu masu hannu a lamarin.
Ya ce, "Daga rahotannin da jami'ai na suka samu, mutum daya tak ya mutu amma wasu masu tarin yawa sun samu raunuka kuma suna asibiti ana duba su."
A wani labari na daban, wani dan ta'adda wanda ya addabi fasinjojin jiragen ruwan kogin Bonny da ke Port Harcourt a jihar Rivers, Dan Ezekiel George, ya shiga hannun 'yan sanda, tare da yaransa bayan sun kai wa wasu fasinjoji hari, har wani mutum ya rasa ransa.
Wanda ake zargin, mai shekaru 28 dan asalin Asarama ne da ke karamar hukumar Andoni a jihar Rivers. 'Yan ta'addan sun yi awon gaba da kayan matafiyan a ranar Alhamis da safe, The Punch ta ruwaito.
Wani mutum, wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatar wa da manema labarai cewa fasinjoji da dama sun samu mugayen raunuka sakamakon adduna da wukaken da 'yan daban suka yi amfani da su, har wani ya rasa ransa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng