Yadda Dakarun Sojin Najeriya Suka Yi Bikin Sallah a Fagen Daga a Borno
- Shugaban sojin saman Najeriya ya taya dakarun soji murnar Sallah a sansanin NAF da ke Maiduguri domin nuna goyon baya
- Ya bayyana muhimmancin sadaukarwa da biyayya da ake tunawa da su a lokacin Sallah, yana mai jinjina wa jaruntarsu a fafutukar yaki da ’yan ta’adda
- Ana ganin wannan ziyara ta kara dankon zumunci da karfin gwiwa ga dakarun da ke bakin fama a Arewa maso Gabashin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Shugaban sojin saman Najeriya, Hasan Bala Abubakar, ya gudanar da bukukuwan Sallah da dakarun NAF a Maiduguri.
Abubakar da shugaban umarnin rundunar dabarun NAF (TAC), Patrick Obeya ya wakilta ya taya dakarun murnar Sallah tare da yabawa da jajircewarsu wajen kare Najeriya daga ta’addanci.

Asali: Twitter
Legit ta tattaro bayani kan yadda sojojin suka yi bikin sallah ne a wani sako da rundunar sojin saman Najeriya ta wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Patrick Obeya ya ce bikin Sallah na Eid-el-Kabir yana koyar da darussa na sadaukarwa da biyayya.
Ya ce hakan ne ginshikin aikin soja, yana mai cewa sojojin saman sun taka rawa sosai wajen rage karfin ’yan ta’adda a yankin.
An yaba da kokarin soji a Arewa maso Gabas
A jawabin da aka gabatar, Patrick Obeya ya bayyana cewa sojojin saman Najeriya da ke aiki a Arewa maso Gabas sun yi namijin kokari wajen kawo saukin matsalar tsaro.
Patrick Obeya ya ce sojojin sun yi kokari ne ta hanyar manyan hare-hare da suka dakile ayyukan mayakan Boko Haram da ISWAP.
Ya ce:
“Jaruntarku da jajircewarku na haifar da babban sauyi. Ina kira da ku ci gaba da wannan kwazo har sai mun murkushe dukkan abokan gaban Najeriya gaba ɗaya.”
Patrick Obeya ya tabbatar cewa nasarorin da aka samu a Damboa, Marte, Izge da Bitta na nuna irin tasirin haɗin kai da ake samu tsakanin rundunonin tsaro daban-daban.
Sojoji na ci gaba da hadin gwiwa da hukumomi
Obeya ya ce haɗin gwiwa tsakanin sojojin sama da sauran hukumomin tsaro kamar rundunar ƙasa da ta ruwa na ci gaba da samar da nasarori a yaƙin da ake yi da masu tayar da zaune tsaye.
Ya kara da cewa irin wannan haɗin kai ya sa ake samun sauyi wajen gudanar da aiki, inda aka samu sakamako mai kyau a hare-haren da aka kai a wurare da dama a yankin.

Asali: Twitter
Ya ce rundunar za ta ci gaba da yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da an cimma nasarar da ake bukata wajen dawo da zaman lafiya.
Bukukuwan Sallah sun karfafa gwiwar sojoji
Ziyarar da bukukuwan Sallah da aka gudanar a sansanin sojin sama a Maiduguri sun kara tabbatar da cewa manyan shugabanni na rundunar na kula da jin dadin kanana.
Haduwar ta kara jaddada ƙimar ƙawance, hadin kai da rundunar sojin sama ke mutuntawa, tare da tabbatar da cewa ana kula da jin dadin dakarun da ke bakin aiki.
Sultan ya nemi a yi addu'an kan tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su cigaba da addu'a kan matsalolin tsaro.
Sarkin Musulmi ya ce matsalar 'yan Boko Haram a Arewa maso Gabas da 'yan bindiga a Arewa ta Yamma sun kai su sanya a yi addu'a ta musamman.
Legit ta rahoto cewa Sultan ya yi kiran ne ga 'yan Najeriya yayin da aka shiga kwanaki masu alfarma na watan Zul Hijja na bana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng