Rashin Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Yi Kira ga 'Yan Najeriya game da Ranar Arafa
- Sarkin Musulmin Najeriya, Sa’ad Abubakar III, ya bukaci Musulmai su yi addu’o’i domin samun mafita ga matsalolin da ke addabar ƙasar nan
- Ya bayyana haka ne a wani jawabi na musamman da aka fitar a madadinsa, yana mai cewa Ranar Arafa na da matuƙar daraja a wajen Allah
- Mai alfarman ya jaddada bukatar addu’a kan matsalolin tsaro irin su Boko Haram da 'yan bindiga a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya shawarci al’ummar Musulmi da su yi addu’o’i masu ƙarfi a yau Alhamis.
Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi kiran ne kasancewar yau ce Ranar Arafa, rana mafi daraja a cikin kwanakin aikin Hajji.

Asali: Facebook
Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa Sarkin ya fitar da wannan kira ne ta bakin babban sakataren ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), Farfesa Khalid Aliyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa addu’o’in da za a yi a wannan rana za su iya jawo rahamar Allah da kuma mafita ga matsalolin da ƙasa ke fuskanta, musamman rashin tsaro da sauran ƙalubale rayuwa.
Ranar Arafa rana ce mai falala inji Sultan
A cikin sanarwar, Sarkin ya bayyana cewa ranar Arafa tana daga cikin ranaku mafi ƙima a wajen Allah SWT.
Baya ga haka, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce yin azumi a wannan rana yana share zunuban da suka gabata da kuma na gaba idan Allah ya yarda.
Ya jaddada cewa Zul Hijja wata ne mai albarka, kuma ya kamata Musulmai su ƙara kusanci da Allah ta hanyar kyawawan ɗabi’u da kuma yawaita addu’a, musamman a ranar Arafa.
Sarkin Musulmin ya ce lokaci ya yi da Musulmai za su hade da zuciya ɗaya wajen neman taimakon Allah kan matsalolin da ke damun ƙasa, ciki har da hauhawar farashi da rashin tsaro.
Arafa: Sultan ya bukaci addu'a kan tsaro
Alhaji Sa’ad Abubakar ya lissafa wasu daga cikin matsalolin da ke damun Najeriya kamar dawowar hare-haren Boko Haram a Arewa maso Gabas.
PM News ta rahoto cewa ya bayyana cewa bayan Boko Haram, akwai matsalar ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta Tsakiya.

Asali: Facebook
Ya ce addu’ar Musulmai a irin wannan rana mai albarka na da tasiri wajen neman gafara da sauƙin fitintinu da suka dabaibaye rayuwar al’umma a ƙasar nan.
Ya kuma roƙi al’umma da su dage da roƙon zaman lafiya, kwanciyar hankali da hadin kai domin wanzar da cigaba da daidaito a tsakanin al’umma.
Ayyukan da ake son yi a ranar Arafa
A wani rahoton, kun ji cewa Legit ta tattaro wasu ayyuka na musamman da ake so kowane Musulmi ya mayar da hankali a kansu a ranar Arafa.
A ranar Arafa ana son duk Musulmin da ba ya cikin dawainiyar aikin Hajji ya yi azumi domin falalar da ke cikinsa.
Baya ga azumi ana so Musulmi ya mayar da hankali game da yin addu'o'i a ranar Arafa, karatun Kur'ani da sauransu.
Asali: Legit.ng