'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Masallaci, Sun Sace Limami da Masallata
- ’Yan bindiga sun afka wa wani masallaci a garin Bushe na ƙaramar hukumar Sabon Birni, inda suka sace akalla mutum 10, ciki har da liman
- Rundunar ’yan sandan Sokoto ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa ana kokarin ceto mutanen da 'yan bindigar suka sace
- Wani dan majalisar dokokin jihar ya yabawa sojoji bisa hana ’yan bindigar yin garkuwa da karin mutane bayan sun kai mummunan harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun kai farmaki wani masallaci da ke yankin Bushe a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
Maharan sun afka wa masallacin ne a lokacin da jama’a ke tsaka da yin sallar Asuba, inda suka yi awon gaba da wasu daga cikin masu ibada.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100

Asali: Original
Jaridar Punch ta wallafa cewa dama mutanen yankin sun dade suna fama da hare haren 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ahmed Rufai ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa jami’an tsaro na iyakar kokarinsu domin ganin an kubutar da wadanda aka sace.
An kai hari masallaci a jihar Sokoto
Wani mazaunin garin Bushe ya tabbatar da cewa ’yan bindigar sun farmaki masallacin ne da sassafe a ranar Alhamis, inda suka yi garkuwa da mutane 10.
Cikin mutanen da aka sace har da limamin masallacin, lamarin da ya jefa jama’ar yankin cikin fargaba da damuwa.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shafe tsawon lokaci suna aikata barna ba tare da samun wata tangarda ba.
Duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin, mazauna garin sun koka cewa harin ya nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar al’ummomin karkara.
Rundunar ’yan sanda ta magantu
Kakakin ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa ana gudanar da bincike don ceto wadanda aka sace.
DSP Ahmed Rufai ya kara da cewa rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro tana aiki tukuru domin tabbatar da cewa an kubutar da mutanen ba tare da wata matsala ba.
A cewarsa, kwamishinan ’yan sanda ya umarci dakarun rundunar su kara kaimi wajen dakile ayyukan ’yan bindiga a yankin.
Daily Trust ta rahoto cewa DSP Rufai ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro hadin kai domin ganin an dakile ire-iren wadannan hare-hare a yankin.
Dan majalisa ya yabawa jami’an tsaro
Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar yankin, Sa’idu Ibrahim, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa akalla mutum 10 aka yi garkuwa da su.
Sai dai ya jinjinawa sojojin da ke aiki a yankin bisa matakin da suka dauka wanda ya hana maharan yin awon gaba da karin mutane.
Ya ce dole ne a dauki kwararan matakai domin kawo karshen hare-haren da suka addabi yankin Sabon Birni da sauran sassan jihar.
Mazauna yankin sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen yaki da ’yan bindiga domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
'Yan bindiga sun sace Manjo Janar Tsiga
A wani rahoton, kun ji cewa mazauna yankin Tsiga sun bayyana yadda 'yan ta'adda masu garkuwa suka sace tsohon shugaban hukumar NYSC.
An ruwaito cewa 'yan bindiga sama da 100 ne suka taru yayin da aka sace Manjo Janar Maharazu Tsiga da wasu karin wasu mutanen garin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng