Hadaka: Da Gaske an Hango Atiku Tare da Namadi Sambo da Yemi Osinbajo?
- Ana shirin gudanar da bikin nadin sabon Sarkin Ijesaland, Oba Clement Adesuyi Haastrup, a birnin Ilesa da ke jihar Osun
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya samu tarba daga wani mutum mai kama da Yemi Osinbajo a filin jirgin sama
- An yi ce-ce-ku-ce kan mutumin, wasu na cewa da gaske Yemi Osinbajo ne wasu kuma na cewa ba shi ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - A ranar Asabar 25 ga Mayu 2025, birnin Ilesa da ke jihar Osun zai cika da taron jama’a yayin bikin nadin sabon sarkin Ijesaland, Oba Clement Adesuyi Haastrup, Ajimoko III.
Ana sa ran cewa bikin zai samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Asali: Facebook
Atiku ya wallafa a X cewa an tarbe shi cikin girmamawa a filin jirgin sama na Akure yayin da yake kan hanyarsa zuwa bikin nadin sarkin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da gaske Osinbajo ya hadu da Atiku?
A cikin hotunan da Atiku Abubakar ya wallafa, an hango wani mutum mai kama da tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo cikin masu tarbarsa.
Sai dai binciken Legit Hausa ya gano cewa mutumin ba Yemi Osinbajo ba ne, sunan shi Dr Bode Ayorinde.
Dr Bode Ayorinde shi ne mai jami'ar Achievers da ke Owo kuma tsohon dan majalisar wakilai ne daga jihar Ondo.
Ganin mutumin mai kama da Osinbajo da Namadi Sambo tare da Atiku Abubakar waje daya ya kara jawo ce-ce-ku-ce a siyasar Najeriya kasancewar ana maganar hadakar 'yan adawa.
Atiku da manyan baki za su taru a Ilesa
Bikin nadin sarautar Owa Obokun na Ijesaland zai janyo dubban jama’a da manyan baki daga sassa daban-daban a ciki da wajen Najeriya.
Oba Clement Adesuyi Haastrup shi ne sarki na 41 da zai rike sarautar Owa Obokun, kuma ana kallon nadinsa a matsayin wata muhimmiyar alama ta cigaba da daidaita al’ada a yankin.
An shirya bikin a babban dandalin taron birnin Ilesa inda ake gudanar da jerin taruka na al’adu da rantsar da sabon sarki cikin martaba da kima.
Hukumar NSCDC ta dauki tsauraran matakai
Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Osun ta tabbatar da cewa ta girke jami’an tsaro da dama a yankin domin tabbatar da tsaro da kare lafiyar jama’a da manyan baki.
Tribune ta wallafa cewa kakakin hukumar, ASC Kehinde Adeleke, ya bayyana cewa an tura jami’an sintiri da suka riga suka mamaye wurin taron don hana duk wata barazana.
Kwamandan NSCDC na jihar, Igbalawole Sotiyo, ya gargadi masu shirin tayar da hankali da su nesanta kansu daga wurin.

Asali: Twitter
Igbalawole Sotiyo ya bukaci jama’a su bada hadin kai domin ganin an gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali.
An ce jami’an tsaro sun kasance cikin shiri tun yau Juma’a, inda suka fara sintiri a manyan hanyoyi da wuraren taron domin dakile duk wata matsala.
Omokri ya yi fatan daidaita Atiku da Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya ce yana fatan daidaita Atiku Abubakar da Bola Tinubu.
Reno Omokri ya ce zai cigaba da girmama Atiku Abubakar duk da cewa ya yanke matsayar goyon bayan Bola Tinubu a 2027.
Omokri ya yi maganar ne bayan wani mai bibiyarsa a kafar sada zumunta ya tambaye shi dalilin rashin caccakar Atiku Abubakar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng